Wata kotun daukaka kara mai zaman kanta a birnin Yola ta Adamawa ta tabbatar da Aishatu Dahiru Binani a matsayin halastacciyar ‘yar takarar gwamnan jihar a karkashin jam’iyyar APC.
Kotun da mai shari’a Tanko Yusuf Hassan ya jagoranta ta yi watsi da hukuncin wata kotun tarayya da ta soke takarar Aishatu Binani ta sanar da cewa APC ba ta da dan takara a zaben 2023.
A lokacin sanar da hukuncinsa, alkalin ya umarci a mika sunan Binani ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, a matsayin ‘yar takarar gwamnan APC a Adamawa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp