Shugabar kotun daukaka kara, Mai Shari’a Monica Dongben-Mensem, ta bayyana cewa kotun ta zartar da jimillar hukunce-hukunce 7,295 da kuma ci gaba da sauraron kararraki 3,665 a kakar shari’a ta 2022/2023.
Da take jawabi yayin bikin fara sabuwar shekarar shari’a a Abuja, Mai Shari’a Dongben-Mensen, ta tunatare da cewa an samar da kwamitoci 98 domin sauraron koke-koken zabe a fadin kasar nan, saboda a gudanar da jimillar korafe-korafen zabe guda 1,209 da aka shigar a gabanta.
- Cibiyar Kimiyyar Noma Na Sin CATAS Ta Cancanci Yabo
- Babu Wata Yarjejeniya Tsakaninmu Da Gwamnatin Tarayya Kan Dakatar Da Yajin Aiki – NLC
Ta ce daga cikin korafe-korafen, biyar an shigar da su ne a kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa kuma an kammala su, yayin da wasu 147 da aka shigar a kotun sauraron kararrakin zaben sanatan, sannan an gabatar da kararraki 417 na zaben majalisar wakilai.
Shugabar kotun daukaka kara ta ce, jimillar korafe-korafe 557 da ke da alaka da majalisar dokokin jihohi, da kuma zabukan gwamnoni 83 ne aka yi watsi da su. Ya ce jihohi 28 ne suka halarci zaben gwamnoni kuma an shigar da kara a jihohi 24.
A cewarta, a halin yanzu sashin Abuja na cike da tarin takardu, sannan kuma suna fama da rashin isassun wuraren ajiya da ofisoshi.
Shugabar ta yi kira ga ministan Babban Birnin Tarayya Abuja da ya samar da wani katafaren fili don gina sashin kotun da ke Abuja.
A nasa jawabin, Ministan Shari’a, Prince Lateef Fagbemi ya ce gwamnatin Shugaba Bola Tinubu za ta magance matsalar karancin alkalai a kotun daukaka kara da kuma kotun koli.
Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike ya hori bangaren shari’a da su ci gaba da rike amanar jama’a saboda ‘yan Nijeriya na da kwarin gwiwa kan hukuncin kotuna.
Wike ya yi wannan kiran ne a taron shekara shari’a ta 2023/2024 na kotun daukaka kara, wanda aka gudanar a shalkwatan babban kotun daukaka da ke Abuja.