Kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja ta yi zamanta na farko kan sauraren karar da gwamnan jihar Kano, Abba K. Yusuf ya shigar kan hukuncin da kotun sauraron kararrakin zabe ta jihar ta yanke na tsige shi daga kujerar gwamna da tabbatar da Dr. Nasiru Gawuna a matsayin wanda ya yi nasara.
Idan dai baku manta ba, kotun sauraren korafe-korafen zaben Gwamnan Kano mai alkalai uku a karkashin mai shari’a Oluyemi Akintan Osadebay ta tsige Abba K. Yusuf daga kujerar gwamnan Kano a ranar 20 ga watan Satumba, 2023, bayan kotun ta zare kuri’u 165,663 da ta ce ba su cika ka’idar zama halastattun kuri’u ba.
- DA DUMI-DUMI: Kotu Ta Kori Gwamna Abba Gida-Gida Ta Tabbatar Da Nasarar Gawuna
- NNPP Ta Yi Watsi Da Hukuncin Kotun Sauraren Karar Zaben Gwamnan Kano Da Ta Ba Gawuna Nasara
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta sanar da Abba Yusuf wanda a matsayin wanda ya lashe zaben ranar 18 ga Maris, 2023, inda ta ce ya samu kuri’u 1,019,602 inda ya doke Gawuna na APC da kuri’u 890,705.
Sai dai jam’iyyar APC ta tunkari Kotun, bisa zargin tafka kura-kurai da magudin zabe.
Kotun ta karbi korafin da APC ta shigar inda ta soke zaben Yusuf, da dalilan cewa sama da kuri’u zabe 160,000 INEC ba ta sanya hannu da tambari da kwanan wata ba.
An rage kuri’un Yusuf zuwa 853,939 yayin da kuri’u 890,705 Ganuwa suke a yadda suke tun asali.
Daga bisani gwamnan ya shigar da kara a gaban kotun daukaka kara.
Jam’iyyun APC da INEC, da NNPP su ma sun shigar da kara a gaban kotun.
A ranar Litinin, babban lauyan gwamnan, Wole Olanipekun SAN (wanda shi ne babban lauyan Tinubu a PEPC), ya bukaci kotun daukaka karar da ta ajiye hukuncin da kotun sauraren korafe-korafen zabe ta yanke a baya.
Olanipekun ya bayar da hujjar cewa kotun sauraren korafe-korafen zaben gwamnan ta kirkiro wasu sabbin sharudda wadanda suka fita daga dukkan hukunce-hukuncen da kotun daukaka kara ko kotun koli ta yanke.
Dangane da batun kuri’un zabe kuwa, ya ce wannan shi ne karo na farko a tarihin kotun da wata kotu za ta soke zabe kan rashin sanya hannu a bayan kuri’un zabe.
Olanipekun ya bayar da hujjar cewa bai kamata a bar hukuncin da kotun sauraren korafe-korafen zaben gwamnan ta yanke ba.