Kotun Koli ta dage karar da wasu gwamnonin jihohi suka shigar kan kalubalantar Gwamnatin Tarayya na aiwatar da sabon tsarin canjin takardun kudi.
Kotun Kolin ta dage Shari’ar zuwa ranar 3 ga watan Maris din 2023.
- Mahara Sun Tarwatsa Gidan Rediyon Dan Majalisar Da Ke Goyon Bayan Atiku A Ribas
- Dan Majalisa Ya Sauya Sheka Daga APC Zuwa PDP A Jigawa
Idan za a iya tunawa dai babban bankin Nijeriya (CBN) ya tsawaita wa’adin aiwatar da tsarin canjin takardun kudade na 200, 500 da naira 1,000 daga 31 ga watan Janairun zuwa 10 ga watan Fabrairun 2023 biyo bayan korafe-korafen da wasu ‘yan Nijeriya suka yi ta yi.
Amma Kolin bayan karar da wasu Gwamnoni suka shigar da Gwamnatin tarayya da gwamnan CBN tare da bankunan kasuwanci, kotun ta umarci dukkanin bangarorin da su dakatar daga aiwatar da shirin har zuwa lokacin da za a saurari batun a ranar 22 ga watan Fabrairun.
Kodayake, daga baya shugaban kasa Muhammadu Buhari a yayin jawabin da ya yi wa al’ummar Nijeriya a ranar Alhamis, ya umarci babban bankin Nijeriya CBN da ya sake fitar da tsoffin takardun kudade na naira 200 zallla na tsawon kwanaki 60 don ya sake shiga cikin al’umma tare da sabon takardar kudi na 200 da 500 da 1000.
Sannan Buhari ya ce tsoffin takardun kudade na 500 da 1000 sun tashi a aiki a kasar nan.
Sai dai bayan matakin na shugaban kasa wasu sun dukufa wajen sukar matakin musamman Gwamnonin jam’iyyar APC.
Wasu da suka fito balo-balo suka kalubanci shirin na canjin Kudi sun hada da gwamnoni, Nasir El-Rufai (Kaduna), Abubakar Badaru (Jigawa), Rotimi Akeredolu (Ondo), Umar Ganduje gwamna a jihar (Kano); Kakakin Majalisar Dokokin tarayya, Femi Gbajabiamila; karamin ministan kwadago, Festus Keyamo; da wasu jiga-jigai a jam’iyyar APC.
Manyan Lauyoyin Najeriya kamar Femi Falana da Mike Ozekhome ma sun caccaki matakin shugaban kasar, su na masu cewa bai kamata matakin na Buhari ya iya soke na kotun kolin kasar ba.
Kazalika, wasu karin Gwamnonin Kaduna da Zamfara da Kogi sun sake shigar da wata karar domin kalubalantar Abubakar Malami, ministan shari’a da gwamnan babban bankin Nijeriya, Godwin Emefiele bisa kin mutunta umarnin kotun koli kan tsoffin takardun kudade.