Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayyana haramcin sanya siket da Hukumar NYSC ke yi ga ƴan mata masu bautar ƙasa a matsayin saɓawa ‘yancin addini da kuma kundin tsarin mulki na 1999.
Shari’ar dai ta samo asali ne daga ƙorafe-ƙorafen da wasu tsofaffin wasu ƴan NYSC biyu suka shigar gaban kotu, waɗanda suka haɗa da Miss Ogunjobi John Blessing da Miss Ayuba Vivian, ta hannun lauyoyinsu, Baba Shehu Ahmad da K.A. Lawal. An haɗe shari’ar biyu saboda suna da kamanceceniya ta fuskar doka. Hukuncin wanda Mai shari’a, Hauwa Joseph Yilwa ta yanke.
- Gwamna Radda Ya Gargadi Ƴan NYSC Kan Shiga Ƙungiyoyin Asiri
- Minista Ya Nemi A Mayar Da NYSC Shekaru 2
A cikin kunshin hukuncin, Mai shari’a Yilwa ta ce, tilasta wa ƴan mata sanya wando a matsayin wajibcin tufafi yana tauye ‘yancin yin addini da mutunci da kundin tsarin mulki ya tabbatar musu da shi.
Masu ƙarar sun bayyana cewa tilasta musu saka wando ya ci karo da addininsu na Kirista, inda suka jingina da Littafin Kubawar Shari’a 22:5, wanda suke fassara cewa ya haramta wa mata sa kaya irin na maza.
Kotun ta yanke hukunci cewa haramcin sanya siket saboda dalilan addini ba bisa doka ba ne, kotun ta karɓi kokensu gaba ɗaya, waɗanda da suka haɗa da:
- Umarnin NYSC ta amince da sanya siket ga mata masu hujjar sanya wa saboda addininsu.
- Umarnin NYSC ta dawo da su ta ‘yan matan da suka shigar da ƙarar tare da ba su takardar shaidar kammala NYSC.
- Kotun kuma ta bayar da umarnin bai wa kowacce daga cikinsu kuɗaɗe har ₦500,000 a matsayin diyya saboda tauye musu ‘yancin su.
Kotun ta kuma bayyana cewa cin zarafi da muzantawar da suka fuskanta daga hannun jami’an NYSC ya ci karo da ‘yancinsu na yin addini da bayyana shi a aikace.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp