A jiya Litinin shugaban kasar Sin ya kaddamar da taron koli na mata na duniya a birnin Beijing, inda ya gabatar da jawabi tare da shawarwari 4 na kasar Sin kan inganta ci gaban harkokin mata a duniya. Jawabin na shugaba Xi ya ja hankalin mahalarta da ma jama’ar duniya inda suke ganin ya aza wani sabon tubalin hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa a bangaren raya harkokin mata.
Wannan taro a ganina, ya zo a daidai lokacin da ake bukatarsa. Bayan shekaru 30 da cimma yarjejeniyar Beijing da ta zama jigo wajen raya harkokin mata, an samu sabbin sauye-sauye a duniya wadanda ke bukatar sabbin dabaru. Kuma haduwar da aka yi a yanzu, zai kara ba mata a duniya kwarin gwiwa da bayyana musu cewa, suna da makoma mai haske. Baya ga haka, zuwan mahalartan kasar Sin zai nuna musu irin ci gaban da Sin ta samu a fannin domin su dauki darasi.
Kasar Sin ta bayar da gagarumar gudunmawa ga raya harkokin mata a duniya, inda take zurfafa musaya da hadin gwiwa a fannonin da suka shafi mata domin taimakawa mata a kasashe masu tasowa inganta rayuwarsu da cimma burikansu. Misali, ta horar da mata sama da 200,000 daga kasashe da yankuna sama da 180, baya ga shirye-shiryen horar da mata sama da 100 da ta aiwatar a kasashe masu tasowa.
Idan muka dawo cikin gida, za mu fahimci furucin shugaba Xi cewa, “kowacce mace tauraruwa ce a sabon tafarkin zamanantar da kasar Sin” domin kasar tana iyakar kokarinta wajen tabbatar da daidaiton jinsi cikin dukkan manufofinta na kasa da ba mata damar taka rawa daidai da maza. Sin na daya daga cikin kasashen duniya dake da adadin mai yawa na mata ma’aikata, inda suka dauki kaso 40 cikin 100. Mata Sinawa, suna ci gaba da taka rawar gani a dukkan bangarori na rayuwa. Ni ganau ce na yadda mata a yankunan karkara suka tashi tsaye wajen marawa gwamnati baya a yakin da ta yi da talauci da kuma ci gaba da ake yi na ganin hannun agogo bai koma baya ba. Wani babban batu shi ne, yadda ake aiwatarwa da gyara dokoki domin tabbatar da mata sun samu damarmaki iri daya da takwarorinsu maza, daga bangaren ilimi zuwa na mallakar kadarori da gidan aure da zamantakewa da sauransu. Haka zalika a bangaren siyasa, inda ake da mata masu jagorantar hukumomi da kwamitocin siyasa a kasar.
Shawarwarin shugaba Xi Jinping, abu ne da kasa da kasa za su iya aiwatarwa domin an yi a Sin kuma kwalliya ta biya kudin sabulu. Za mu iya cewa, wannan taro ya sake samar wa duniya karin kafa ta hadin gwiwa domin tattaunawa da hada karfi da karfe wajen gaggauta samar da ci gaba mai ma’ana a fagen kare hakkokin mata da goya musu baya wajen taka rawar gani a harkokin da suka shafi bunkasa tattalin arziki da zamantakewa da ma bayar da gudunmawa ga ci gaban duniya. (Fa’iza Mustapha)