Muhammad Bello Matawalle, tsohon gwamnan Jihar Zamfara kuma Ministan Tsaro na Ƙasa na yanzu, ya yi gargaɗi ga abokan hamayyarsa da su daina haɗa shi da ayyukan Bello Turji, wani shahararren shugaban ‘yan bindiga a jihar. A wata sanarwa da ofishinsa ya fitar ranar Lahadi, Matawalle ya zargi wasu daga cikin gwamnatin Jihar Zamfara da ƙalubalantar yanayin tsaro domin ƙirƙirar labaran karya da nufin jefa shi cikin maganar.
Matawalle ya mayar da martani ne ga wani bidiyon sauti da ke yawo a shafukan sada zumunta wanda ke nuna cewa yana da alaƙa da aiyukan ta’addanci a Jihar Zamfara. Ya nuna yatsan zargi kan gwamnatin jam’iyyar PDP mai mulki a halin yanzu, inda ya zarge ta da ƙoƙarin bata masa suna.
- Matsalar Tsaro: Gwamnatin Zamfara Ta Sanya Dokar Takaita Zirga-zirgar Ababen Hawa
- Matsalar Tsaro: Ɗalibai Sun Ƙaurace Wa Ɗakunan Kwana A Lakwaja
Haka kuma ya zargi wasu da ya bayyana a matsayin makiyan ci gaban Zamfara da Najeriya, waɗanda ya ce sun yi adawa da nadin sa a matsayin Ministan Tsaro na Ƙasa da Shugaba Bola Tinubu ya yi. Matawalle ya jaddada cewa ya samu dukkanin takardun izinin tsaro daga hukumomin da suka dace kafin a tabbatar da nadin sa, yana mai jaddada niyyarsa ta yin aiki da gaskiya.
Matawalle ya jaddadacewa yayi shugabanci cikin tawali’u, gaskiya da adalci a lokacin mulkinsa na gwamna. Ya yi kira ga jama’a da su ƙi yarda da bidiyon sautin da ke yaɗuwa, yana bayyana shi a matsayin ƙoƙarin ɓata masa suna da aka shirya.