Gwamnatin tarayya ta yi kira ga ‘yan jarida da su guji yada labaran da ba su dace ba musamman na ‘yan ta’adda, ‘yan fashi da sauran masu aikata miyagun laifuka da ke barazana ga zaman lafiya da tsaron kasar nan.
Da yake jawabi a taron manema labarai karo na bakwai na 2025 na ministoci da aka yi ranar Laraba a Abuja, Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa, Mohammed Idris, ya jaddada muhimmiyar rawar da kafafen yada labarai ke takawa wajen tsara tunanin jama’a tare da tallafawa kokarin tsaron kasa.
- An Kama Amarya Kan Zargin Kashe Mijinta Bayan Kwana 9 Da Aurensu A Kano
- Tattalin Arzikin Sin Tamkar Teku Ne Ba Karamin Tabki Ba
“Kafofin watsa labarai, a matsayin masu tsaron ƙofa kuma abokan haɗin gwiwar gina ƙasa, suna da muhimmiyar rawar da za su taka wajen tallafa wa namijin kokarin sojojinmu ta hanyar bayyana nasarorin da suka samu,” in ji shi.
“Dole ne mu daina tallata miyagun ayyukan ‘yan ta’adda. Dole ne mu cire su daga jerin shafukan manyan labarai na jaridunmu, mu rahoto ayyukansu a matsayin masu aikata laifuka, sannan mu kore labaran karya.”
Ministan ya jaddada cewa, kungiyoyin ta’addanci da masu aikata laifuka sukan yi amfani da kafafen yada labarai da shafukan sada zumunta don yada tsoro, yada labaran karya, domin samun sabbin mabiya.
A saboda haka, ya bukaci ‘yan jarida da editoci da su rungumi dabi’ar kishin kasa wajen bayar da rahoto ta hanyar guje wa kanun labarai masu daukar hankali ga farfagandar ta’addanci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp