Nasir S Gwangwazo">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home LABARAI

Ku Kiyayi Jita-jita Domin Ba Mu Daukar Ma’aikata, Cewar INEC

by Nasir S Gwangwazo
January 5, 2021
in LABARAI
2 min read
Ku Kiyayi Jita-jita Domin Ba Mu Daukar Ma’aikata, Cewar INEC
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Hukumar Zabe ta kasa (INEC) ta yi kira ga jama’a da su yi watsi da wani labari da ake yadawa wai ta na daukar mutane aiki.

Mista Festus Okoye, Babban Kwamishina kuma Shugaban Yada Labarai da Wayar da kan Masu Zabe na hukumar, shi ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya bayar a ranar Juma’a a Abuja.
Okoye ya ce a yanzu dai INEC ba ta daukar kowa aiki, ya kara da cewa tun tuni aka dakatar da daukar sabbin gama jami’a da kwararrun ma’aikata.
Ya ce: “INEC na so ta kara jawo hankalin jama’a zuwa ga aikin da wasu jami’an karya ‘yan damfara su ke yi na daukar aiki na jabu.
“’Yan damfarar sun bude gidajen yana na karyar daukar aiki inda su ke karbar kudade a hannun jama’ar da ba su ankara ba har su na ba su takardun kama aiki na bogi da sunan Hukumar.
“Idan za a iya tunawa, tun a ranar 30 ga Mayu, 2020, Hukumar ta bada wata sanarwa inda ta ja hankalin jama’a kan yaduwar wasu takardun kama aiki na karya da aka ce wai sun fito daga gare ta ne.
“Mun sanar da jama’a lokacin cewa Hukumar ta dakatar da shirin ta na daukar ma’aikata. Mun shawarci kowa da kowa da ya yi watsi da duk wata ji-ta-ji-ta game da daukar aiki da raba takardun kama aiki da aka ce wai daga Hukumar ne su ka fito, kuma mun sanar da hukumomin tsaro wannan damfarar.”
Okoye ya ce wannan Hukuma dai amanar jama’a ce wadda ke gudanar da aikin ta a bisa tsarin da aka amince da shi na aiki tsakani da Allah kuma a bayyane.
Ya ce wannan tsari na yin aiki a bayyane shi ya sanya a duk lokacin da hukumar ke daukar ma’aika ake yayatawa.
Okoye ya ce, “Mu an kara jan hankalin jama’a da su san dabarun da ‘yan damfara ke amfani da su don kada su fada cikin tarkon su na masu aikata laifi.”

samndaads
SendShareTweetShare
Previous Post

NAF Ta Dukufa Wajen Fatattakar Boko Haram A Borno

Next Post

Cibiyar MDD Ta Yaba Yadda Kiristoci Suka Gudanar Da Bikin Kirsimeti Cikin Kariyar Korona

RelatedPosts

Za A Kulle Duk Layin Da Ba A Yi Rijistarsa Da Katin Dan Kasa Ba Ranar 9 Ga Fabrairu

Za A Kulle Duk Layin Da Ba A Yi Rijistarsa Da Katin Dan Kasa Ba Ranar 9 Ga Fabrairu

by Nasir S Gwangwazo
11 hours ago
0

Gwamnatin Tarayya ta kara wa’adin da aka diba wa ’yan...

Sayar Da Kadarorin Gwamnati Zai Taimaki ‘Yan Nijeriya, Inji Minista

Sayar Da Kadarorin Gwamnati Zai Taimaki ‘Yan Nijeriya, Inji Minista

by Nasir S Gwangwazo
11 hours ago
0

Ministar Kudi, Zainab Ahmed, ayau Juma’a, ta ce shirin Gwamnatin...

Zakzaky

Matar Sheikh EL-Zakzaky Ta Kamu Da Korona, In Ji Danta

by Nasir S Gwangwazo
16 hours ago
0

Daga Rabiu Ali Indabawa, Matar Shugaban Kungiyar Musulunci a Nijeriya...

Next Post

Cibiyar MDD Ta Yaba Yadda Kiristoci Suka Gudanar Da Bikin Kirsimeti Cikin Kariyar Korona

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version