Majalisar dokokin jihar Kaduna ta bukaci tsoffin masu rike da mukaman siyasa a gwamnatin Malam Nasir El-Rufai da su shirya kare kansu a wurin hukumomin yaki da cin hanci da rashawa da kuma kotu.
Majalisar ta bayyana haka ne a lokacin da take mayar da martani kan kalaman kare kai da wasu tsaffin masu rike da mukamai a gwamnatin El-Rufai suka yi.
- Jawabin Muller Kan Yin Ritaya Daga Bugawa Kasar Jamus Kwallo
- NPA Ta Kaddamar Da Kananan Jiragen Ruwa Don Saukaka Zirga-zirga A Matatar Man Dangote
A wani taron manema labarai da suka gudanar a Abuja ranar Talata, wasu tsaffin kwamishinonin sun yi suka ne kan rahoton kwamitin majalisar wanda ya zargi wasu daga cikinsu da tsohon gwamnan da karkatar da Naira biliyan 423.
Tsoffin kwamishinonin sun zayyana bayanan kudi daga shekaru takwas na El-Rufai, inda suka bayyana cewa rahoton majalisar na da nasaba da siyasa da nufin bata nasarorin da gwamnatinsu ta samu.
Sun ce yayin da El-Rufai ya dauki matakin shari’a don tabbatar da kare hakkinsa na ‘yancin dan Adam, su kuma dole su fayyace abin da suka kira rahoton da cewa, “son kai da nufin bata musu suna”.
Sai dai a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, shugaban kwamitin binciken kuma mataimakin kakakin majalisar dokokin Kaduna, Barista Henry Magaji ya yi tir da “kokarin da tsofaffin masu rike da mukaman siyasar suka yi na boye zarge-zargen da ake yi na wawure dukiyar jihar da kuma almubazzaranci da dukiyar a shekarun gwamnatinsu”.
A cewarsa, taron manema labarai da tsoffin kwamishinonin suka yi bai wuce zarge-zargen da ba su da tushe balle makama da kuma kasa magance babban batu wanda shi ne dumbin dukiyar jihar da aka wawure.
Talla