Gwamnatin Tarayya ta ce ta bai wa kowace jiha daga cikin jihohi 36 na Nijeriya da kuma babban birnin tarayya Abuja, tirelar shinkafa 20 domin raba wa talakawa.
Ministan yada labarai, Mohammed Idris ne, ya bayyana hakan bayan kammala taron majalisar zartarwa (FEC), na ranar Litinin.
- Sin Ta Fadada Manufar Yada Zango A Kasar Ba Tare Da Biza Ba Zuwa Karin Tashoshi
- Wasan Karta Na Joe Biden Game Da Xizang Ya Gaza Tun Kan Ya Fara
Ya ce kowace tirela tana dauke da buhun shinkafa 1,200 mai nauyin kilogiram 25 kuma an mika su ga gwamnonin jihohi a yunkurin rage radadin da talakawa suke ciki na karancin abinci da tsadar rayuwa.
Gwamnatin Tarayya ta ce tana fatan gwamnonin jihohin za su raba kayan abincin ga mabukata a matakin jiha da kananan hukumomi.
Ana dai fama da tsadar kayan abinci da ake alakantawa da matsalolin tattalin arziki wanda janye tallafin mai da matsalar tsaro suka haddasa.
A gefe guda kuma, ana tunanin gwamnatin ta yi haka ne domin tausar zukatan wasu matasan Nijeriya da ke shirye-shiryen tsunduma zanga-zanga kan matsin rayuwa.