Karamin Ministan Kwadago, Festus Keyamo, ya ce, kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta na gudanar da yajin aiki a halin yanzu ne sakamakon yarjejeniyar da suka cimma da gwamnati a zamanin mulkin PDP a 2009.
Keyamo wanda ya gana da ‘yan jarida, kan yajin aikin na ASUU, ya ce ‘yan Nijeriya kawai su tuhumi PDP ba gwamnatin APC da ke mulki a halin yanzu ba.
- Takarar Musulmi 2: Magoyan Bayan APC Sun Yi Zanga-zanga A Legas, Sun Bukaci A Sauya Shettima
- An Shawarci Manoman Jihar Kaduna Su Rika Biyan Basussukan Bankuna
Kakakin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC, ya zargi gwamnatin PDP da gazawa wajen cika alkawuran da suka cimma da ASUU tun a 2009.
Ya yi ikirarin cewa daga tsakanin 1999 zuwa 2015 da PDP ta mika wa APC mulki, kungiyar ASUU ta shiga yajin aiki har sau 12 da ya ci kwanaki 900 cikin yajin aiki.
“Menene matsalar ASUU a yanzu? Damuwarsu da bukatunsu sun shafi yarjejeniyar da suka cimma ne da gwamnatin PDP a 2009. Sun yi yarjejeniya da ASUU amma sun kasa cikawa. Mun gaji yarjejeniyar ne kuma muka dukufa wajen sake fahimtar juna da su.
“Ba wai muna tura musu sukar ba ne; muna kokarin dakile matsalar ne. Tsakanin 1999 da 2015 lokacin da APC ta amshi ragamar mulki, ASUU ta shiga yajin aiki har sau 12. Na lissafa zai kai kwanaki 900,” ya ce..