Hukumar Kula da Yanayi ta Nijeriya (NiMet) ta gargadi ‘yan Nijeriya da su kasance cikin shiri don samun sauyin yanayi da kuma matsanancin yanayi sakamakon sauyin da yanayin zai haifar.
Darakta-Janar na NiMet, Farfesa Charles Anosike ne ya bayyana hakan a wani taron wayar da kan ‘yan jarida da kungiyoyin farar hula (CSOs) ta gudanar na kwana daya a Abuja.
- Kotu Ta Yanke Wa Ɗan TikTok Tsulange Hukuncin Ɗauri Kan Shigar Zubar Da Mutunci
- Dutsen Da Amurka Ta Jefa Ya Fado Kasa
Anosike ya jaddada muhimmiyar rawar da kafafen yada labarai ke takawa wajen isar da bayanan kimiyya ga jama’a tare da lura da cewa nasarar hukumar ta dogara ba kawai ga daidaiton hasashenta ba har ma da ingantacciyar sadarwa.
Babban daraktan NiMET ya bayyana matakan da aka dauka na baya-bayan nan don inganta ayyukan ba da sabis, ciki har da horar da ma’aikata da magance matsalolin jin dadin ma’aikata da kuma karfafa wa mahalarta damar yin aiki tare da raba ra’ayoyi, aiki zuwa manufa guda na sanya Nijeriya ta fi dacewa, da shirye-shirye, da kuma juriya ta fuskar yanayi.
Taron na da niyyar karfafa hadin kai tsakanin NiMet, ‘yan jarida, da kungiyoyin jama’a, karfafa su da ilimi da kayan aikin da suka dace don yada mahimman bayanai na yanayi ga jama’a.
Har ila yau, da yake jawabi, mai gudanar da taron, Bonabenture Melah, ya ce makasudin tattaunawar shi ne, inganta dabarun sadarwa, da inganta fassarar bayanai, da samar da hadin gwiwa tsakanin kwararru a NiMet da ‘yan jarida, ta yadda ‘yan jarida za su yi aiki yadda ya kamata.
Har ila yau, darektan Sabis na Hasashen Yanayi (DWFS) a NiMET, Farfesa Bincent Weli, ya lura cewa, “sauyin yanayi na da tasiri kai tsaye a rayuwarmu ta yau da kullum.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp