Kudaden kasafin kudi na kasar Sin da gwamnatoci ke samu sun karu da kashi 0.8 bisa dari a mizanin shekara-shekara zuwa kusan yuan triliyan 18.65, kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan 2.63, a cikin watanni 10 na farkon shekarar 2025, kamar yadda bayanan da ma’aikatar kudin kasar ta fitar a yau Litinin suka bayyana.
Gwamnatin tsakiya ta karbi kusan yuan tiriliyan 8.19 na kudaden kasafin kudin a tsakanin wannan lokacin, inda kasonta ya ragu da kashi 0.8 bisa dari a mizanin shekara-shekara, yayin da kananan hukumomi kuma suka karbi yuan tiriliyan 10.46, inda kasonsu ya karu da kashi 2.1 cikin dari. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
ADVERTISEMENT













