Jimilar kudin asusun ajiya na kasar Sin a ketare ya kai dala triliyan 3.3222 zuwa karshen watan Agusta, inda ya karu da dala biliyan 29.9 ko kaso 0.91, idan aka kwatanta da na karshen watan Yuli.
Hukumar kula da musayar kudi ta kasar Sin ta alakanta karuwar da tasirin sauyin kudi da sauyin farashin kadarori.
Ta kara da cewa, tattalin arzikin kasar Sin na ci gaba da habaka yadda ya kamata, cike da juriya da kuzari, da samar da goyon bayan mai karfi ga asusun ajiyar kasar na ketare. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)