Jami’an Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) sun kama Osang Usie Otukpa, wani dan Nijeriya da ake zargi ya damfari wasu ‘yan kasar Australia 139 Dala miliyan 8 ta hanyar kudin Kirifto.
An kama wanda ake zargin ne a filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Ikeja a Legas, lokacin da ya fito daga kasar Amurka.
- Yahaya Bello Ya Samu Beli Bayan Cika Sharudan Kotu
- EU Ta Ware Euro Miliyan 1 Don Tallafa Wa Wadanda Ambaliyar Ruwa Da Kwalara Suka Shafa A Nijeriya
A cikin wata sanarwa da aka fitar, shugaban sashen yada labarai da wayar da kan jama’a na EFCC, Dele Oyewale, ya bayyana cewa Otukpa ya yi amfani da lakabi da dama, da suka hada da Ford Thompson, Oscar Donald Tyler, Michael Haye, Jose Bitto, da Kristin Dabidson, domin aiwatar da wannan zamba.
Ayyukan damfara sun ta’allaka ne a kan wani dan damfara na cryptocurrency mai suna Likuid Asset Group, wanda Otukpa ya habaka sosai a kafafen sada zumunta. An kwadaitar da wadanda aka damfara zuwa saka hannun jari a dandalin, wanda ya haifar da hasarar kudi mai yawa.
Hukumar EFCC ta bayyana cewa an shigar da kudaden da aka samu daga wannan badakalar zuwa asusun bankin Otukpa ta hanyar dandalin musayar cryptocurrency na duniya.
Sanarwar ta ce: “Hukumomin EFCC sun kama wani da ake zargi da damfara ta intanet, Osang Usie Otukpa, bisa zargin damfarar wasu ‘yan kasar Australia 139 da suka kai Dalar Amurka 8,000,000.
“An kama shi ne a filin tashi da saukar jiragen sama na Murtala Mohammed, Ikeja, Legas, bayan isowarsa daga kasar Amurka a ranar Juma’a 6 ga watan Disamba, 2024.
“Otukpa, wanda yake da synaye biyar da suka hada da-Ford Thompson, Oscar Donald Tyler, Michael Haye, Jose Bitto, da Kristin Dabidson – ya zambaci mutanen ta hanyar jawo su a kan kafofin yada labarun don saka hannun jari a dandalin sa hannun jari na cryptocurrency, Likuid Asset Group.
“An karkatar da kudaden zuwa asusun ajiyarsa ta hanyar dandalin musayar cryptocurrency na duniya.”
Oyewale ya ci gaba da cewa, ana ci gaba da gudanar da bincike, kuma za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala aikin. Wannan ci gaban ya bayyana kokarin da EFCC ke yi na murkushe masu aikata laifuka ta intanet da kuma dawo da amana ga tsarin hada-hadar kudi a duniya.