Kudirin dokar da ke neman haramta amfani da kudaden kasashen waje a Nijeriya ya tsallake karatu na farko a majalisar dattawa.
Kudirin dokar mai taken “kudirin doka wajen sauya dokar Babban Bankin Nijeriya na shekarar 2007, mai lamba 7, don haramta amfani da kudaden waje kamar biyan albashi da sauran abubuwan da suka shafi haka,” shugaban kwamitin majalisar dattawa, Sanata Ned Nwoko ne ya dauki nauyin kudirin.
- Babu Wata Sana’a Da Take Da Daukaka Da Samu Irin Harkar Fim – Hajara Usman
- Dangote Ya Yabi Tinubu Kan Tasirin Yarjejeniyar Musanyar Fetur da Naira
An ruwaito cewa kudirin dokar da aka gabatar a zauren majalisar dattawa na da nufin tabbatar da biyan duk wasu kudade da suka hada da albashi da sauran hada-hadar kudi ta hanyar amfani da kudin gida wato naira.
A cewar Sanata Nwoko, yawaitar amfani da kudaden kasashen waje a cikin tsarin hada-hadar kudi na kasar nan na kawo cikas ga darajar naira, wanda hakan yana kawo kalubalen tattalin arziki.
Dan majalisar ya bayyana yadda ake amfani da Dala da ‘Pound Sterling’, da sauran kudaden kasashen waje wajen hada-hadar kasuwanci a Nijeriya a matsayin wani abu na mulkin mallaka da ke ci gaba da kawo cikas ga ‘yancin cin gashin kan Nijeriya.