Shugaba Tinubu ya ce, manufofin da gwamnati ke bi a halin yanzu sun dau hanyar samar da ingantaccen tsarin tattalin arziki da zaman lafiya.
Wata sanarwa da Mista Dele Alake, mai baiwa shugaban kasa shawara kan ayyuka na musamman, sadarwa da dabaru, ya bayyana a ranar Talata a Abuja.
- Tinubu Ya Gana Da Tawagar Kamfanin Man Fetur Na Shell
- Tinubu Ya Yi Ganawarsa Ta Farko Da Hafsoshin Tsaro
Ya ce Shugaban ya ce, gwamnati na kan hanyar samun nasara duk da kalubalen da kasar ke fuskanta.
Yayin da yake karbar bakuncin jami’an bankin Amurka da suka kai ziyara, shugaban ya kara da cewa kasar ba ta da wani dalili na gazawa a kasashen nahiyar Afirka.
Ya ce gwamnati ta himmatu wajen samar da sauye-sauye da za su samar da ci gaba mai dorewa da ci gaban kasa.
“Mun yi imanin muna kan hanya madaidaiciya zuwa yanzu. Kuma muna bukatar duk taimakon da za mu iya samu,” in ji Shugaban.
Tinubu ya bukaci mahukuntan bankin su bayar da goyon baya da hadin guiwa da gwamnati domin ci gaban moriyar juna ga Nijeriya da cibiyoyin hada-hadar kudi.
Ya ce ba za a iya magance kalubalen shugabanci da ci gaban da kasar ke fuskanta ba sai an yi gyare-gyaren da suka shafi kudi da na hukumomin da ke hada-hadar kudade.