Kudurin kirkiro ‘yansandan jihohi ya samu nasarar tsallake karatu na biyu a zauren majalisar wakili, wanda ke neman gyara kundin tsarin mulkin Nijeriy domin bayar dama kowacce jiha ta mallaki ‘yansandanta.
Kudurin da ya samu goyon bayan mataimakin shugaban majalisar wakilai da sauran ‘yan majalisa 14, wanda a yanzu haka yana wurin kwamitin gyaran kundin tsarin mulki na majalisa, sai dai kuma wasu ‘yan majalisan sun ki amincewa da shi, inda suke ganin cewa gwamnoni za su yi amfani da shi a matsayin makamin samun nasarar siyasarsu.
Da yake jagorantar muhawaran kan kudurin, dan majalisar APC daga Jihar Kwara, Tolani Shagaya ya bayyana cewa kudurin dokar kirkiro ‘yansandan jihohi zai sake dawo da tsarin shugabanci na gaskiya tare da seta jihohin kasar nan wajen magance matsalar tsaro da ta addabi kasar nan.
Ya ce samar da ‘yansandan jihohi shi ne ya fi muhimmanci na yadda za a dakile matsalar rashin tsaro a tsakanin al’umma da ke fadin kasar nan da yaki da miyagun laifuka a tsakanin jama’a.
Ya ce a halin yanzu, ‘yansandan jihohi sun rika sun kasance a wasu sassan, domin akwai irinsu Amotekun da Neighborhood Watch. Ya kara da cewa kudurin yana neman kwai a ba su hurumin doka da kuma barin su gudanar da ayyukansu bisa tsarin dokokin kasa.
Da yake goyon bayan kurudin bayan tsallake karatu na biyu, dan majalisan APC daga Jihar Borno, Ahmed Jaha ya ce kafa rundunar hadin gwiwa ta farar hula a Jihar Borno ya taimaka matuka wajen yaki da Boko Haram da rage musu karfi wajen gudanar da ayyukansu.
Ya ce idan har wadannan rundunar hadin gwiwa ta farar hula suka kasance wani bangare na ‘yansanda a jihohi, to za a samu saukin tattara bayanan sirri. Ya ce ba aikin soja ba ne ya kawo tsaro a cikin kasa, amma saboda gazawar samar da harkokin tsaro a cikin kasa ya sa suka sha.