Yayin da firaministan kasar tsibiran Solomon Manasseh Sogavare yake hira da wakiliyar babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG, ya yi nuni da cewa, kulla dangantakar diplomasiyya da Sin, daya ne daga cikin kudurori mafi dacewa da kasar tsibiran Solomon ta tsaida a tarihi.
Ya kuma yabawa gwamnatin kasar Sin bisa nasarorin da ta samu wajen kawar da talauci, kana yana fatan inganta karfin samun bunkasuwar kasarsa ta hanyar hadin gwiwa da Sin.
Ya kuma soki wasu kasashen dake daukar ma’auni biyu da tsoma baki kan harkokin cikin gidan sauran kasashe. Kana ya bayyana damuwa sosai ga batun zubar da ruwan dagwalon nukiliyar Japan cikin teku, yana mai cewa, idan akwai matsala to bai kamata a zubar da ruwan ba. Kuma wannan shi ne ra’ayin kasar tsibiran tekun Pasifik. (Zainab)