Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya bayyana cewa a kullum sai ya yi magana da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu sau biyu kan matsalar tsaro da ke addabar jihar.
Uba Sani ya shaida hakan ne a lokacin da ke ganawa da wata gidan talabijin dan-gane da matsalolin tsaro da suke addabar jiharsa.
- Nijeriya Ce Kan Gaba Wajen Lashe Kyaututtuka A Wasannin Kasashen Yammacin Afirika Na Bana
- Tarihin Masarautar Zazzau Da Sarakunanta (1)
A ranar 8 ga watan Maris, ‘yan bindiga 100 sun mamayi makarantar firamare da karamin sakandarin ta Kuriga a karamar hukumar Chikun ta Jihar Kaduna, inda suka yi garkuwa da dalibai 312 da shugaban makarantar Abubakar Isah.
Sannan, a daren ranar Lahadi, ‘yan bindigan sun sake yin garkuwa a kalla mutane 86 a Tantatu da Aguba da ke gundumar Kufana a karamar hukumar Kajuru da ke Jihar Kaduna.
Amma a hirarsa, Gwamna Sani ya ce, ya shaida cewa Tinubu da shugabannin hukumomin tsaro sun dukufa wajen ganin sun kawo karshen matsalar tsaro a Ni-jeriya baki daya.
Ya ce, “Mai girma shugaban kasa ya damu matuka. Na kan yi magana da shuga-ban kasa sau biyu kullum kan wannan lamarin kuma ya nuna damuwarsa sosai. Ya sanya azama da himma wajen ganin an samu nasarar kawo karshen matsalar nan. Ina da yakinin jami’an tsaro su ma za su yi iyakan bakin kokarinsu wajen dakile matsalar nan.
“Mun ganawa da mai bai wa shugaban kasa shawara kan lamuran tsaro (NSA) da shugabannin hukumomin tsaro dukkaninsu kowa ya nuna damuwarsa. Mai girma shugaban kasa ya damu shi ma. Sau biyu yake kirana kullum, wani lokacin ma har sau hudu yake kirana a rana, domin ya tambayeni kan halin da ake ciki a jihata. Ba na ko shakka tare da azama da himma gami da irin salon jagorancinsa zai iya kai-wa ga karshen wannan matsalar. Kawai batu ne na lokaci.”
Uba Sani ya kuma ce gwamnatinsa a shirye take wajen ganin ta taimaka wa al’ummar jihar ta yadda za su tsayuwa da kafafunsu a bangaren kasuwanci da sauran harkokin rayuwa.