ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tarihin Masarautar Zazzau Da Sarakunanta (1)

by Idris Aliyu Daudawa
2 years ago
Zazzau

Babban tushe mafi mahimmanci ga farkon tarihin Zazzau shine tarihin da aka kirkira a farkon karni na 20 daga al’adun baya.Yana ba da kuma labarin gargajiya ne na kafuwar masarautun kasar Hausa daga jarumin al’adu Bayajidda,kuma ya ba da jerin sunayen masu mulki tare da tsawon lokacin da kuma suka yi sarauta.Dangane da wannan tarihin, an ce asalin masarautar hausa ko Habe ta fara ne tun daga karni na 11, wanda Sarki Gunguma ya kafa. (1) Wannan majiyar kuma ta sanya ta zama daya daga jihohin Bakwai.

Mafi shaharar sarautar Zazzau ita ce Sarauniya (ko kuma Gimbiya) Amina, wacce ta yi mulki ko dai a tsakiyar karni na 15 da tsakiyar na 16, kuma Muhammed Bello ne ya rike ta, masanin tarihin Hausa a karni na 19 kuma Sarkin Musulmi na biyu, shine farkon wanda ya kafa daula a tsakanin Hausawa(2).

Zazzau ta kasance wurin tattara bayi ne don a kai su  zuwa kasuwannin Arewacin Kano da Katsina, inda ake musayar su da gishiri tare da ‘yan kasuwar da ke jigilar su zuwa Arewacin Sahara.(3) Dangane da tarihi a cikin littafin, an gabatar da addinin musulunci ga masarautar a wajen shekara ta 1456, amma ga alama ya bazu a hankali, kuma tsafin arna ya ci gaba har zuwa lokacin da Fulani suka ci shekara ta 1808.A wasu lokuta a tarihinta,Zazzau ta kasance tana karkashin kasashen makwabta irin su Songhai, Bornu da kuma Kwararafa.(4) Wannan karin rubutu da aka sa bai daidaitu  ba domin a kwai tsallaken zance a dukkanin sakin layin. Zazzagawa an same su da addinin musulunci kuma Shehu Usmanu ya tabbatar da hakan.Tun asali kasar Zazzau ba su da maguzawa.

ADVERTISEMENT

Masarautar Gidan Fulani

A watan Disamba na shekara ta 1808 babu Fulani a cikin wadanda Shehu Usmanu Danfodiyo ya turo su da su kifar da ko su fidda Sarkin Zazzau Muhammadu Awwal Makau daga kasar Zazzau, illah kinibibin da ya kullu a tsakanin Malaman da suke zaune a kasar Zazzau.Wannan ya biyo bayan hijirar da Sarkin Kano Muhammadu Al-wali ya yi bayan kashe shararren Malamin nan malam Dan Zabuwa wanda ya ke shima bafillace ne. Ganin haka Fulani su kai gangami wajen tuntsurar da mulkinsa. Sarkin Kano ya yi kaura zuwa kasar Zazzau,a lokacin mulkin Sarkin Zazzau Muhammadu Awwal Makau a  cikin shekara ta 1807 amma bai samu hurumin zama ba. Duk da cewar shi suruki ne ya ke ga Sarkin Kano Muhammadu Al-wali.Wannan hijira ta Sarkin Kano

LABARAI MASU NASABA

Tarihin Shugaban Makaranta Na Farko A Arewa Hedimasta (2)

Cin Amana Uku Da Suka Sauya Tarihi A Duniya

Muhammadu Al-wali  ita ta kawo cece-kuce a kasar Zazzau inda a karke ya kawo karken mulkin Sarkin Zazzau Muhammadu Awwal Makau. Inda gaurayen kabilun Malaman da ke zaune a kasar suka hada kai suka kifar da mulkinsa bayan ya tafi masallacin Idi don gabatar da  Karamar sallah .

Domin ta wannan dalilin ne ya sa shi tilasa ya bar kasar Zazzau inda ya kafa kasar Abuja kuma a halin yanzu ita ce aka kafa hedikwatar kasar nan.Kuma masarautar ta sauya da sunan sarki Sulaimanu Barau watau Suleja. Kalmar Fulani ta samu ne dalilin Shehu Usmanu.Amma malaman kabilun da ke zaune su ne: kabilar Mande a yau a na kiransu Mallawa,Barebari, Sullubawa da kuma Katsinawa.

Mun samo daga Wikipedia Hausa

Zazzau
Idris Aliyu Daudawa
+ postsBio
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Tarihin Rayuwar Galadiman Kano Alhaji Tijjani Hashim (2)
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Kyamar Baƙi: An Sake Kwaso Ƴan Nijeriya 83 Daga Afirka Ta Kudu
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Kamfanin Simintin Dangote Ya Tallafa Wa Manoma 60 Da Kayan Aiki A Edo
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Tsohon Shugaban Ƙasa Jonathan Ya Ƙaddamar Da Ayyukan Raya Ƙasa 18 A Jihar Bauchi

MASU ALAKA

Laifukan Intanet: Kotun Abuja Ta Karɓi Rahoton DSS, Ta Ba Da Belin Wani Ɗan Gwagwarmaya
Tarihi

Tarihin Shugaban Makaranta Na Farko A Arewa Hedimasta (2)

May 30, 2026
Cin Amana Uku Da Suka Sauya Tarihi A Duniya
Tarihi

Cin Amana Uku Da Suka Sauya Tarihi A Duniya

February 22, 2026
Tarihin Sarkin Zazzau Ja’afaru Dan Isiyaku 1936-1959
Tarihi

Tarihin Sarkin Zazzau Ja’afaru Dan Isiyaku 1936-1959. (2)

January 11, 2026
Next Post
Nijeriya Ce Kan Gaba Wajen Lashe Kyaututtuka A Wasannin Kasashen Yammacin Afirika Na Bana

Nijeriya Ce Kan Gaba Wajen Lashe Kyaututtuka A Wasannin Kasashen Yammacin Afirika Na Bana

LABARAI MASU NASABA

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

September 10, 2026
’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

September 10, 2026
2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

September 10, 2026
Zabe: Gwamnatin Kano Ta Taƙaita Zirga-zirgar Mutane Da Ababen Hawa

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

September 10, 2026
Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.