Kugiyar Northwest Progressives Forum (NPF) ta yi watsi da cece-kucen da ake yi kan zabar tsohon gwamnan jihar Jigawa, Mohammed Badaru a matsayin ministan tsaro Nijeriya, inda ta ce shugaba Bola Tinubu ya dasa kwarya a gurbinta.
Da yake jawabi a taron manema labarai da aka gudanar a Kaduna a ranar Laraba, Daraktan Sadarwa na kungiyar Adamu Isa, ya bayyana cewa, ya kamata masu sukar bai wa Badaru mukamin minista su yi biyayya ga hukuncin shugaba Tinubu.
- Me Ya Sa Nijeriya Ke Neman Shiga Tsarin BRICS?
- Wagner Yevgeny Prigozhin Ya Mutu A Hatsarin Jirgin Saman Rasha
Isa ya ce: “Shugaba Tinubu ya cancanci a yaba masa kan wannan mataki da ya dauka, duba da irin yadda Badaru yake da ban mamaki.”
Kungiyar ta bayyana cewa a lokacin da yake rike da mukamin Gwamnan Jihar Jigawa, ya bai wa sha’anin tsaro fifiko, hakan ta sa ya yi nisa a harkokin tsaro.
Da yake karin haske game da cancantar Badaru ya bayyana cewar tsohon gwamnan ba ya bukatar horon soji don gudanar da aikinsa yadda ya kamata.
Adamu ya jaddada cewa tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya rike mukamin a baya kuma ya taka rawar gani a wancan lokaci.
NPF ta nuna farin cikinta kan rahotannin da ke cewa Badaru ya riga ya hada tawagar kwararru domin taimaka masa wajen gudanar da ayyukansa a matsayin babban ministan tsaro.
Adamu ya tabbatar da cewa, wannan mataki na taka-tsantsan yana kara jaddada kyakkyawan hangen nesa da basirar Badaru na hada tawaga mai inganci.
An kuma bayyana fahimtar kungiyar game da manufofin tsaron kasa, inda ta lissafo muhimman abubuwa da suka hada da tabbatar da shirye-shiryen rundunar sojojin Nijeriya ta kasa, ta ruwa da ta sama, daidaita makamai da ma’aikata don bukatun tsaro, da kuma ba da fifikon jin dadin dakarun soji ta hanyar bada horo.
NPF ta bayyana muhimmancin inganta fagen tsaron kasar nan don rage dogaro da kasashen ketare da tabbatar da hadin gwiwar tsaro a shiyyar da duniya baki daya.
Adamu ya kara da cewa, “Mun yi imani cewa nada Mohammed Badaru a matsayin ministan tsaro zai kawo sauyi mai tasiri.”
A karshe kungiyar ta bayyana kudirinta na marawa Badaru baya a aikinsa na kasa tare da yin alkawarin ci gaba da yi masa addu’a don samun nasara.