Ƙungiyar wayar da kai da tallafa wa ‘yan Ɗariƙar Tijjaniya ta Nijeriya, ‘Tijjaniya Grassroot Mobilization and Empowement Initiative of Nigeria (TIGMEN) ta yi kira ga Rundunar sojojin ƙasar nan da su gaggauta binciken harin da aka kai wa masu bikin Maulidi na Tudun Biri, tare da hukunta waɗanda suka kai harin.
TIGMEN ta bayyana haka ne a wani taron manema labarai da ta kira a ranar Larabar da ta gabata a ofishin ta da ke Kaduna, wanda shugaban ƙungiyar, Sayyadi Nasiru Shaikh Bello ya gabatar, tare da sauran shugabanninya.
- Tudun Biri: Garin Harin Bam, Ya Shekara Fiye Da 200 Babu Asibiti Da Makarantar Boko
- Kamfanonin Jirage Za Su Fara Biyan Tarar Jinkirta Tashi Da Soke Tafiya
Haka kuma ƙungiyar ta yi kira da a kafa wani ƙwaƙƙwaran kwamitin da zai kula da raba taimako da gudunmawoyin da ake samu don ganin abin ya kai ga waɗanda suka cancanta. Ta kuma yi kira da cewa a tabbatar an raba gudunmawar cikin adalci da gaskiya.
Kungiyar ta kuma nemi a bayyana sakamakon kwamitin da aka kafa don binciken wannan lamari, aƙalla makwanni biyu bayan kafa shi. Inda ta ce, wajibi ne a biya diyyar waɗanda suka rasa rayukan su a wannan hari.
Tun farko a jawabin nasa, Sayyidi Nasiru ya bayyana cewa sun kafa wannan ƙungiya ta su ta TIGMEN ne don jawo hankali, wayar da kai, ilimantarwa, girmamawa da tallafa wa mabiya ɗarikar Tijjaniyya a duk faɗin Nijeriya.