Mataimakin ministan kasuwanci na kasar Sin (MOC) Wang Shouwen ya ziyarci kasar Amurka daga ranar 2 zuwa 5 ga watan Afrilu bisa gayyatar da bangaren Amurka ya yi masa, kana ya jagoranci taron mataimakan ministoci karo na farko na kungiyar hada-hadar kasuwanci da cinikayya ta kasashen Sin da Amurka, tare da mataimakiyar sakatariyar kasuwancin Amurka mai kula da cinikayyar kasa da kasa madam Marisa Lago, a cewar MOC a yau Jumma’a.
Wang ya ce, kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da Amurka don aiwatar da matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma, da karfafa tuntubar juna, da fadada hadin gwiwa, da daidaita sabani ta hanyar kungiyar hada-hadar kasuwanci da cinikayyar, da samar da yanayi mai kyau ga kamfanonin kasashen biyu don su yi hadin gwiwar cinikayya da zuba jari.
Ya kara da cewa, bangarorin biyu sun amince da tallafawa ayyukan bunkasa kasuwanci da zuba jari da bangarorin biyu suka shirya, da ayyukan hadin gwiwa a fannin fasahar makamashi mai tsafta da kiwon lafiyar mata, da lalubo hanyoyin inganta hadin gwiwar yin cinikayya cikin sauki, da karfafa tuntubar juna da mu’amala a fannin kayyade fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje. (Yahaya)