Islamic First Aid Organization” (JIFAO) da ke babban birnin tarayya Abuja ta gabatar da taron kara wa juna sani a karo na hudu.
Kungiyar hadaka na ‘yan agajin dukulallen kungiya ce wacce ta hada da kungiyoyin agaji da suka hada da na Jibwis mai shalkwata a Abuja da Jibwis da ke da shalkwata a garin Jos na Jihar Filato da Fityanul Islam of Nigeria da Jama’atu Nasrul Islam da An’nahada da Ash’shabab da kuma Initiatibe.
- Bayan Hukuncin Kotu, Dan Takarar Sanata Na APC A Nasarawa Ya Bai Wa Magoya Bayansa Hakuri
- Ba Zan Yi Kewar Barin Mulki Ba Saboda Kushe Ni Da ’Yan Nijeriya Ke Yi Duk Kokarina —Buhari
‘Yan agajin sun samu horo a kan abubuwa da yawa masu matukar muhimanci da suka hada da ayykan agaji shi kansa da zamantakewa da dogaro da kai da neman ilimin addini da na zamani da muhimancin hadin kan al’umma da dai sauransu.
Taron ya samu gudummuwar wasu jami’an gwamnati da kuma masu zaman kansu domin kara sanin makaman aiki. Daga cikin hukumomin da suka bayar da gudummuwar sun hada da rundunar ‘yansandan Nijeriya da hukumar kiyaye hadura da hukumar farin kaya (DSS) da hukumar shigi da fice da hukumar Cibil Defence da hukumar gyaran hali da dai sauransu.
‘Yan agaji sun tabbatar da sun samu horo a wannan haduwa mai inganci, kuma sun shaida cewa wannan karon abin ya za musu kamar shi ne na farko saboda yadda aka karantar da su.
Kungiyar Jibwis da ke Abuja karkashin jagorancin, Sheikh (Dr) Abdullahi Bala Lau ita ce ta zo ta daya a gasar fareti da aka yi a wannan hadakar, domin sun buga kafa kai ka ce sojoji ko ‘yansandan Nijeriya ne.
Shugaban JIFAO, Alh. Ahmad Adamu Jingi ya yi kira ga gwamnatin tarayya idan ta tashi daukan ma’aikata musamman a bangaren tsaro ta rika neman ‘yan agaji domin suna da kwarewa a kan harkar tsaro sosai duba da yadda ake koyar da su wannan fannin.
Daraktan Jibwis a Abuja, Alhaji Umar Isma’il wanda ya kasance kwamatan JIFAO, ya ja hankalin ‘yan agaji da su ci gaba da nuna halin da’a kamar yadda aka san su da shi, su kuma dage wajen aiki da abin da aka karantar da su domin samun nasara a wajen Allah.
Taron ya samu halartar manyan malamai da daraktoci gami da sarakuna har ma da sauran al’umma da suka hada da Draktan kungiyar Izala, Alhaji Ahmad Lau da Shugaban majalisar malamai na Abuja, Sheikh Muhammad Auwal mai Gaskiya da
Alh. Abdullahi Abdullmalik Diggi da Sarkin Bwari, Alhaji Muhammad Awwal Musa Ijakoro ll.