Wata kungiyar rajin kare dimokuradiyya, mai kare shirin sabunta fata na shugaba Tinubu (the Renewed Hope Interest Defenders), a ranar Laraba, ta yi na’am da shirye-shiryen sauye-sauyen tattalin arziki na Shugaba Bola Tinubu, ciki har da cire tallafin man fetur, farfado da matatun mai na cikin gida, dokokin da aka zartar da nufin bunkasa zuba jari a bangaren mai da iskar gas.
Sai dai kungiyar ta bukaci a gaggauta dakatar da shugaban kamfanin man fetur na kasa (NNPCL), Bayo Ojulari.
Shugaban kungiyar, Obed Agu, wanda ya yi jawabi a wani taron manema labarai a Abuja, ya ce, zaman bitar ayyuka zango na uku ya nuna cewa manufofin Tinubu na da “nufin samar da ci gaba mai dorewa ta hanyar samar da mai mai rahusa, sauke farashin kayayyaki da kuma kyakkyawan fatan samun daidaiton tattalin arziki.”
Sai dai ya zargi shugaban na NNPCL da shirin zagon-kasa kan duk wannan kyawawan manufofin na Tinubu.
A cewar kungiyar, Ojulari ya yi watsi da tattaunawa kan wani rancen dala biliyan 5 na kasar Saudiyya da shugaban kasa ya lalubo a watan Nuwamba 2023, domin ci gaba da aikin gyaran matatar mai ta Fatakwal duk da cewa tana aiki da kashi 60 cikin 100.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp