An karrama Gwamna Abba Yusuf na jihar Kano da lambar yabo ta ‘NUT Golden Award’ saboda bajintar da ya nuna wajen inganta harkar ilimi a jihar.
An bayar da kyautar ne a yayin bikin ranar malamai ta duniya 2024 a dandalin ‘Eagle Square’ da ke Abuja, wanda aka shirya tare da hadin gwiwar ma’aikatar ilimi ta tarayya.
- Mantuwa Na Matukar Taimakon Rayuwar Mutane – Masani
- Yadda Na Kirkiro ‘Brain-chip’ Da Ke Dawo Wa Wadanda Aka Haifa Da Makanta Ganinsu – Elon Musk
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bature Dawakin Tofa ya fitar a Kano ranar Asabar.
Shugaban NUT na kasa, Titus Ambe, ya yaba da sadaukarwar Yusuf don ciyar da ilimi gaba, musamman ta hanyar tallafawa jin dadin malamai da ci gaba da horar da rasu.
Yusuf ya jaddada kudirinsa na kara saka hannun jari a fannin ilimi, inda ya jaddada mahimmancin ci gaba da dorewar ci gaban al’umma domin ganin al’umma masu zuwa za su ci gaba.