Adadin ababen hawa marasa matuka masu shawagi a sama na farar hula na kasar Sin (UAVs) da aka yi wa rajista ya zarce miliyan 1.7, kamar yadda kungiyar masana’antu ta ababen hawa masu shawagi kusa da doron kasa wato LAIA ta bayyana a taronta na shekara-shekara a ranar Litinin.
Wadannan jirage marasa matuka dai sun yi tafiyar sama da sa’o’i miliyan 19.46 a cikin watanni 8 na farkon shekarar 2024, wanda ya karu da kashi 15.6 cikin dari bisa na shekarar da ta gabata, a cewar kungiyar ta LAIA wacce ke zaman kanta da ma’aikatar masana’antu da fasahar watsa labaru ta kasar Sin ke jagoranta.
- Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Ya Gabatar Da Jawabin Murnar Shiga Sabuwar Shekara Ta 2025
- Manyan Makarantun Bauchi Sun Tsunduma Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani
Taron ya ce, aikace-aikacen jiragen sama gaba daya, wadanda jirage marasa matuka ke gudanarwa, na ci gaba da fadada a fannonin da suka hada da isar da kayayyaki, da jagoranci a aikin gona da binciken yanayi. Har ila yau, girman masana’antar jiragen sama marasa matuka na kasar Sin yana ci gaba da habaka, inda ya zama wani muhimmin karfi wajen bunkasa tattalin arzikin ababen hawa masu shawagi kusa da doron kasa.
An yi kiyasin darajar tattalin arzikin ababen hawa masu shawagi kusa da doron kasa na kasar Sin ya zarce yuan biliyan 670, kimanin dalar Amurka biliyan 93 a shekarar 2024, inda aka yi hasashen cewa ya zuwa shekarar 2026 zai zarce yuan tiriliyan 1, bisa ga bayanan da hukumar CCID ta fitar. (Mohammed Yahaya)