Darakta Janar ba kungiyar masana’antu na kasa MAN Segun Ajayi-Kadir, ya nuna damuwarsa a kan yadda a zango na hudu na 2024 matsin tattalin arzikin kasar, ke ci gaba da zamowa masu gudanar da masana’antu a kasar, gazaya tsayawa a kan kafafunsu.
Segun, a hirarsa da jaridar The PUNCH ya danganta hauhawan farashin kayan da suke gudanar da ayyukansu, wanda jakan ke janyo masu raguwar kayan da suke sarrafawa.
- Wadanne Sakamako Aka Samu Daga Cinikin Tsakanin Sin Da Kasashen Ketare
- An Kashe Mutane 5 A Wani Sabon Hari A Filato
Kazalika, ya danganta hauhawan kudin ruwa na bankuna, da tsadar man Dizil da karin farashin kudin wutar lantaki, a matsayin manyan da ke ci gaba da zamowa fannin babban kalubale duk da cewa masana’antun kasar, sun samar da gudaunmawar kashi 8.46 ga tattalin arzkin kasar a zango na biyu na 2024.
Sai dai, gudunmawar da masana’antun kasar suka samar ga tattalin arzkin kasar, ta ragu daga kashi 8.62 a zango na biyu na 2023, inda raguwar ta fi kamari a zango na daya na 2024, wadda ta kai kashi 9.98.
Hakazalika, a cikin rahoton kundin da ‘ya’yan kungiyar suka tattara a zango na rabin shekarar 2024, sun koka a kan kaluabalen samun karin kudin ruwa na bankuna.
A watan Satumbar 2024, kwamtin samar da tsare-tsare na bankin CBN, ya kara kudin ruwan zuwa 50, wanda ya kai kashi 27.25 daga kashi 26.25.
Bugu da kari, kusan sau biyar duk a 2024, CBN yana kara kudin ruwan, domin yak are hauhawan farashin kaya a kasar.
Har ila yau, Segun ya danganta tsadar kudin makamashi, a matsayin daya daga cikin kalubalen da fannin ke ci gaba da fuskanta, sai dai ya ce, an dan samu ragi a farashin man Dizili, musamman saboda kaddamar da matatar man Dangote.
Ya sanar da cewa, yarjejeniyar da kamfanin NNPCL da matatar man Dangote suka kulla ta sayar da danyen mai a kan farashin Naira, hakan zai taimaka wajen habaka ayyukan masana’antu a zango na hudu na 2024, wanda hakan zai kara taimakawa, wajen raguwar yin amfani da kudaden musaya na ketare.
Shi kuwa Daraktan cibiyar hada-hadar kasuwanci na masu zaman kansu Muda Yusuf ya bayyana cewa, kalubalen da ake fuskanta na samun kudaden musaya, na ci gaba da zamowa fannin karfen kafa.
Ya sanar da cewa, akasarin masu masana’antu a kasar, sun dogara ne kachokam wajen shigo da kayan daga ketare, inda kuma faduwar darajar Naira, ya haifar masu da tsadar gudanar da ayyuansu.
Ya yi nuni da cewa, idan matatar man Dangote ta iya sayen danyen mai a kan farashin Naira hakan zai samarwa da masana’antun sauki.