Kungiyar ‘Yan Dangwale da ke jihar Kano ta aika wa majalisar dokokin jihar wasika domin sake duba dokar samar da masarautu hudu da kuma sauke dakataccen sarkin Kano na 14 Muhammad Sanusi da aka yi ba bisa ka’ida ba kamar yadda kungiyar ta yi ikirari.
A wata ganawa da Leadership Hausa ta yi da shugaban kungiyar, Najib Abdulkadir, ya ce bukatar ta su ba wani abu ba ne face ganin an dawo da marauratar Kano guda daya rak kamar yadda take a baya.
Sai dai a lokacin da yake karin bayani game da yadda wasikar kungiyar ta tada kura a Kano, ya karyata wasu zarge-zarge da ake yadawa cewa babu kamshin gaskiya a kan su.
Ya ce sun tura ne a kashin kansu domin ganin an dawo da masarautun Kano zuwa daya, wanda suke ganin zai taimaka wajen kawo zaman lafiya da hadin kai.
Najib, ya kara da cewa tun a gwamnatin da ta gabata ta Abdullahi Umar Ganduje suke kai wa majalisar kokensu ta hanyar tura wasika dangane da wannan lamari amma kuma majalisar take nuna halin ko in kula.
A kwanan nan ne dai ake ta ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta kan makomar masarautun Gaya da Rano da Karaye da kuma masarautar Bichi.
Sai dai har izuwa yanzu gwamnatin Kano ba ta ce komai ba a kai ba, sai dai bayan nasarar da Abba Kabir Yusuf ya yi a Kotu a watan Junairu, tsohon gwamnan Kano kuma Jahoran jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya yi tsokaci kan yiyuwar sake duba fasalin masarautun Kano da Ganduje ya yi.