Manyan Lig-Lig na Nahiyar Turai da kungiyar ‘yan wasa Fifpro sun shigar da karar hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA gaban hukumar kasashen Turai kan abin da suka kira ‘mamaye komai’ da hukumar ta yi a ‘yan shekarun nan.
Gasanni Turai da ake bugawa guda 39 ciki har da Premeir Ingila, kungiyoyi 1,130 a fadin kasashe 33, sun yi korafin FIFA na wuce gona da iri karkashin dokar Nahiyar Turai ta shirya gasa, musamman idan ana maganar tsara wasannin kasashe karkashin FIFA duk da cewa gasar La Liga ba ta cikin mambobin gasannin Turai amma ta shiga cikin wannan korafi ita ma.
- An Daure Wani Mutum Shekara Bakwai Bisa Laifin Lalata Yarinya ‘Yar Shekara 11
- An Gudanar Da Zaɓen Ƙananan Hukumomi Cikin Kwanciyar Hankali A Kaduna – Gwamna Sani
Babban daraktan tsare-tsare na FIFPRO, Aledander Bielefeld, ya ce bangarori daban-daban sun shigar da koke gaban hukumar Tarayyar Turai suna kiran abin da wanda ba su yi tsammani ba kuma ya kamata a yi abin da ya dace.
Korafin ‘Yan Wasa Ya Yi Yawa
Akwai turka-turkar da ke faruwa yanzu kan yawan wasannin da ‘yan wasa ke bugawa a kaka, kuma ita ce kara ta baya-bayan nan da aka shigar domin kungiyar kwararrun ‘yan kwallon kafa ita ma ta bi sahun wannan kara kan FIFA a watan Yuni, game da yawan wasannin da ake tsara bugawa.
Kungiyar da ta ‘yan wasan Faransa sun shigar da karar ne a kotun kasuwanci da ke Brussels “suna kalubalantar halarcin hukuncin FIFA na sanya wasannin kasashe musamman kan hukuncin kirkira da sanya kofin duniya a 2025.
An tsara za a samu wakilan Turai 12 a bikin fadada kafin duniya da za a yi a Amurka a 15 ga watan Yuni zuwa 13 ga watan Yuli. A watan Disambar 2022 ne majalisar kolin FIFA ta tabbatar da fadada gasar inda kungiyar ‘yan wasan ta nuna jayayyarta tana cewa “an matse komai ta yadda ‘yan wasa ba za su samu damar hutawa ba yadda ya kamata tsakanin kakar da aka kammala da sabuwa.