A halin yanzu al’ummar Nijeriya da dama sun shiga shirye-shiryen fuskantar abubuwan da za su iya faruwa sakamakon sauya fasalin wasu takardun Naira da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya shirya yi daga ranar 15 ga watan Disamba wanda ake sa ran duk wanda bai sauya takardar kudin zuwa sababbin da aka sauya ba sun zama takaradun iska kenan. Wannan wa’adi da aka sa ne ya sanya mutane da suka boye kudade a wurare daban-daban suka shiga dimuwa tare da daukar matakan ganin ba su yi asara ba.
Binciken jaridar LEADERSHIP Hausa, ya nuna cewa, cikin matakan da masu irin wadannan kudaden suke dauka sun hada da sayen kudaden kasashen waje, wannan rububin sayen Dalar ta sanya a halin yanzu Dalar ta yi tashin gwauron zabi inda ake sayar da Dala 1 a kan fiye da Naira 800 wanda ba a taba ganin irin wannan tashin da Dalar ta yi ba a cikin ‘yan shekarun nan, dabarar ita ce tunda ba za su iya kai dinbin kudaden da suka mallaka ba zuwa banki ba don ajiya to in har suka sayi Dala shike nan ba ruwansu da wani wa’adi da Babban Banki ya sanya.
Wasu kuma masu irin wadannan kudaden sun shiga sayen duk wata kaddara, da wanda zai iya zama musu riba da wanda ma ba zai zama mai kawo riba ba, wani da ya nemi mu sakaya sunansa ya bayyana cewa, akwai wani Attajiri a garin Kaduna wanda a halin yanzu yana sayen duk wata kaddara da aka kai masa talla, “A halihn yanzu ya bude gidan gonarsa inda yake tara motocin da ya saya, zuwa yanzu ya sayi motoci kirar Golf fiye da 70.
A bangaren gwamnoni kuwa, Hukumar EFCC ta sanar da cewa, tana nan ta sanya ido a kan harkokin wasu gwamnoni uku da suka rasa yadda za su yi da kudaden da suka tara sun kuma shirya amfani da biliyoyin kudadn don biyan albashin ma’aikatan jihar a hannu, Shugaban Hukumar, Abdulrasheed Bawa, ya sanar da haka a tattaunawarsa da Jaridar Daily Trust, ya kuma ce, jami’ansa hukumar za su cigaba da kai samame cibiyoyin canjin kudi don bankado masu kamfanonin canjin da suke taimakawa masu batar da sawun kudaden sata, ya kuma nemi al’ummar Nijeriya su taimakawa shirin musamman ganin hakan zai taimakawa dukkan ‘yan Nijeriya ne gaba daya.
Kamar dai yadda aka sani a ranar 26 ga watan Okoba ne Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya sanar da shirinsa na sauya fasalin Naira, ya kuma bayyana cewa, sauya fasalihn zai taimaka wajen daidaita tsarin tattalin arzikin kasar nan zai kuma daga darajar Naira da ta yi warwas a kasuwannin duniya.
Duk da an bayar da damar cigaba da mu’amala da tsofaffin kudaden daga ranar 15 ga watan Disamba har zuwa ranar 31 ga watan Janairu na 2023. Amma ‘yan siyasa, ‘yan kasuwa masu zuba jari da sauran al’umma suna ta gogoriyon kokarin canjin kudaden da suka boye zuwa Dala Amurka da kuma sayen kaddarori, wanda hakan ya tayar da kura a bangaren tattalihn arzikin kasa gaba daya.
Babban Gwamnan Banki (CBN), Godwin Emefiele, ya bayyana cewa, cikin natijar da ake sa ran samu sakamakon wannan canji sun hada da dakile kudaden da ‘yan ta’adda suka tara a cikin daji ta hanyar karbar kudin fansa sakamakon garkuwa da mutane da suka yi, bayani ya nuna cewa, da yawa daga cikin kudaden da ‘yan ta’addan suka tara na can cikin daji sun boye don ba za su iya kaiwa bankuna ba saboda yawansu da kuma ba za su iya bayanin yadda suka tara kudaden ba, al’umma dai na sane da yadda ‘yan ta’adda ke karbar makudan miliyoyin Nairori a matsayin kudaden fansar wadanda suka sace a sassan kasar nan.
Shirin EFCC Na Sa Wa Gwamnoni 3 Ido
A tattaunawar da shugaban EECC, AbdulRashi Bawa ya yi da jaridar Daily Trust ya bayyana cewa, wasu Gwamnonin Nijeriya na neman hanyoyin batar da makudan kudaden da suka taskace suka kuma boye a gidajen gwamnati amma a halin yanzu hukumar ta nan ta sanya ido don dakile duk wani mataki da za su dauka don cimma wannan mummunan manufar, duk ya ki sanar da cikkaken bayani a kan wadannan gwamnoni uku, amma bayanan sun nuna cewa, biyu daga cikin gwamnonin sun fito ne daga bangaren Arewacin Nijeriya yayin da daya Gwamnan ya fito ne daga Kudancin Nijeriya kuma za su bayyana cikakken bayanan da ya shafe su a nan gaba kadan.
Ya ce, bayanan sirri da hukumar ta tattara sun nuna cewa, gwamnonin sun shira shigar da makudan kudaden cikin harkokin hadahadar kudaden kasa ta hanyar biyan albashin ma’aikatan jihohin na su ta tsabar kudi kai staye.
Ya kara da cewa, “duk da bamu san yadda za su cimma wannan aikin ba amma dole mu dakatar da su don yin haka ya saba wa sashi na 2 na dokar Yaki da Ta’annati da Kudaden al’umma na (Money Laundering Prohibition Act), duk da cewa, zuwa yanzu basu biya albashin da tsabar kudin ba amma wannan babbar lamari ne da zamu cigaba da sanya idon hana faruwarsa.
“Doka ta yi cikakken bayani a kan hanyoyin hulda da kudade, doka ta amince da duk wani da za iy mu’amala da kudade to kada su wuce Miliyan 5 ga mutum daya, amma kuma ga wata Kamfani ko wata Hukuma kada kudin ya wuce Naira Miliyan 10, kuma laifi ne yin mu’amala na kudi da ya wuce yadda hukuma ta tsara.
Batar Da Kudaden Haramun Ta Hanyar Sayan Kaddarori
Haka kuma shugaban EFCC ta tabbatar da cewa, suna da bayanai na yadda a halin yanzu wasu masu kudi suke rububin sayayen kaddarori da kudaden da suka boye a wurare daban-daban don ganin sun cimma wa’adin da aka sanya na dole mutane su batar da kudaden ko kuma su yi asarar su gaba daya.
“In har kana son kudadenka su yi daraja dole ka shigar da su Banki daga nan zuwa 31 ga watan Janairu 2023, akan haka muke aiki tare da bankuna muna kuma neman duk wanda yake da wasu bayanai ya gaggauta kawo mata don mu bi sawunsu,” in ji shi.
Za A Cigaba Da Kai Samame Cibiyoyin Canji
Shugaban na EFCC ya kuma bayar da tabbacin cewa za a cigaba da kai samame kasuwanin canji kudaden kasashe waje a fadin tarayyar Nijeriya saboda muhimmancin da ke tattare da bukatar kare shirin da masu boye kudaden ke yi na sayen dala da kudaden wasu kasashen weje.
“Cibiyoyin cannji na da maukar muhimmanci saboda mutane da dama suna amfani da su wajen canza kudaden da suka boye zuwa kudaden kasashen waje, a kan haka suna da matukar muhimmanci.
A kan haka ya yi kira ta musamman ga masu gudanar da canjin kudi da su ba hukumar dukkan goyin bayan da ya kamata don samun nasarar wannan shiri na gwamnati don kuwa al’umma kasa ne za su amfana inhar aka samu nasarar bunkasar tattalin arzikin kasa, ya kuma nemi su kai rahoton dukkan wasu kudade da basu gane musu ba ga ofishin hukumar mafi kusa da su.
An Nemi Al’umma Su Kwantar Da Hankalinsu
Daga karshe Shugaban Hukumar EFCC, AbdulRashid Bawa ya nemi al’umma su kwatar da hankalisu, yana mai cewa, harkar sauya fasalin Naira wani abu ne da Babban Banki (CBN) ke yi daga lokaci zuwa lokaci, ya kuma kamata a ce,an yi wannan csauya fasalin tun a shekara 8 da suka wuce.
“Abin da gwamnati ke bukata anan shi ne al’umma su kai kudaden su banki don ajiya ba kuma tare da sun biya wasu kudade ba. “Ta yaya za a tafiyar da tattalin arziki da kusan kashi 85 na kudaden da ake mu’amala da su suna can a hannun mutane a boye? A daidai lokacin da muke kira da gudanar da tattalin arziki ba tare da mu’amala da kudi ba wato (Cashless Policy) me ya sa al’umma ke boye kudade, me ya sa al’umma basa zuwa bankin don harkokin kudi? Kana da damar amfani da hanyoyi da dama wajen sarrafa kudadenka to me yasa al’umma za su boye kudade ba tare da sun kai banki ajiya ba kamar yadda aka saba? Tambayar da da shugaban EFCC ya yi ke nan a tattaunawarsa da manema labarai a makon jiya.
Kada A Maimaita Abin Da Ya Faru A 1984 – Talakawa
Wasu ’yan kasuwa talakawa sun bayyana cewa, suna nuna tsoro da rashin jin dadinsu ne kan lamarin. Musamman saboda yadda kwatankwancin irin wannan canjin ya jefa al’umma a shekarar 1984 da aka yi a zamanin mulkin Shugaba Buhari na soja, inda al’umma suka tafka asarar miliyoyin Naira. Alhaji Kamal Samaru (Wani dankasuwa) ya bayyana cewa, “Wannan canjin yana iya jefa mutane da dama cikin talauci musamman in suka kasa canza kudaden su a cikin wa’adin da gwamanti ya bayar, a kan haka ya nemi a bar wa’adin a bude, mutane su yi canza kudadensu har a kawar tsofaffin kudin daga zirga-zirga cikin al’umma gaba daya.
Shi kuwa wani ma’aikacin gwamnati da ya bukaci mku sakaya sunansa, ya yi jinjina ne ta musamman ga Shugaba Buhari a kan fito da wannan shiri na sauya fasalin Naira, yana mai cewa, shirin zai karya barayin kudaden gwamanti, wadanda suka taimaka wajen karya tattalin arzikin Nijeriya.
Ya nemi gwamnati da kada ta yi sakosako wajen aiwatar da dokar, ya kuma nemi al’umma su yi hakuri tare da ba shirin goyon bayan da ya kamata don al’ummar Nijeriya za su amfana daga karshe.