Bana shekara ce ta cika shekaru 20 da samar da kaidar “tsaunuka biyu” da shugaba Xi Jinping ya gabatar, inda ya ambaci ruwa mai tsafta da tsaunuka masu kima a matsayin kadarori masu daraja da za a kwatanta su da zinariya da azurfa. Wata kuri’ar jin ra’ayoyin jama’ar duniya da CGTN ta fitar, wadda ta kunshi masu bayyana raayoyi 24,515 daga kasashe 48, ta nuna yadda kasa da kasa suka yi matukar amincewa da manufar “tsaunuka biyu” ta kasar Sin.
Binciken da aka gudanar ya nuna kyakkyawar amincewa da yadda kasar Sin take gudanar da harkokin kula da muhalli da kuma kokarin sauyawa zuwa turbar samar da ci gaba mara gurbata muhalli, wanda hakan ya kara daga martabarta a duniya a matsayin jagora, ginshiki, kuma jajirtacciya wajen kula da shaanin yanayi da muhalli.
Kamar yadda kuriar ta nuna, masu bayyana raayoyin sun amince da nasarorin da kasar Sin ta samu a fannin kula da muhalli, da sauyawa zuwa samar da ci gaba mara gurbata muhalli, inda kashi 68.8 cikin dari suka yaba da kokarin da ake yi na aikin bunkasa gandun daji wajen maido da fadin gandun daji. Kashi 66.5 bisa dari kuma sun jinjina wa dabarun kasar na kafa madatsar iska da inganta yashi wajen yaki da kwararowar hamada, kana kashi 68.9 cikin dari kuma suka tabbatar da rawar da tsarinta na samar da wuraren shakatawa a kasa ke takawa wajen kare muhallin halittu.
Bugu da kari, kashi 70.5 cikin dari na masu bayyana raayoyin sun yaba da yadda kasar Sin ta fadada ayyukan samar da makamashi mai tsafta daga iska, da hasken rana, da dai sauransu, yayin da kuma kashi 69.6 cikin dari suka nuna goyon baya ga kokarin kasar na inganta amfani da makamashi mai tsafta a rayuwar yau da kullum da kuma bangaren sarrafa kayayyaki. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp