Gwamnatin kasar Japan ta amince da buga sabbin littattafan karatu na tarihi, masu kunshe da rage munin laifukan yaki da kasar ta aikata, matakin da ya haifar da nuna matukar rashin gamsuwa daga kasashen Asiya. Sakamakon kuri’un jin ra’ayin jama’a da kafar watsa labarai ta CGTN ta tattara, ya nuna kaso 82.45% na wadanda suka bayyana ra’ayoyinsu daga sassan duniya daban daban, na matukar Allah wadai da halayya, da ayyukan gwamnatin Japan, don gane da batun tarihin kasar na yaki.
Sabbin littattafan da Japan din ta wallafa na kunshe da wasu bayanai da suka sabawa gaskiya, ciki har da karyata cin zarafin mata a yankunan da Japan din ta mamaye, kafin da kuma yayin yakin duniya na biyu.
- Jakadan Sin Dake Amurka: Ana Fatan Amurka Da Sin Su Bi Hanya Daya Don Binciken Yadda Kulla Abota Tsakaninsu
- Masu Zanga-zanga A Nijar Sun Nemi Sojojin Amurka Su Fice Daga Kasar
Sakamakon binciken ya nuna kaso 95.35 na masu bayyana ra’ayoyi sun yi kira ga gwamnatin Japan, da ta martaba batutuwan gaskiya dake kunshe cikin tarihin kasar, suna masu cewa, kamata ya yi a yi saurin ankarar da duniya kan duk wani yunkuri na lullube, ko boye munanan ayyukan da kasar ta aikata, yayin hare-haren da ta kai yankuna daban daban.
Wani mai bayyana ra’ayi yayin neman jin ta bakin jama’a ya ce, “Kamata ya yi kasar da ta aikata sabon nau’in ta’asar kisan kiyashi a tarihi, ta rubuta hakan cikin littafi, kamar yadda hakan ya dace da dokokin kasa da kasa. Kamata ya yi gaskiya ta zamo jigon tarihi, ba wai kwaskwarimar editoci ba.”
An wallafa neman jin ra’ayin jama’ar na CGTN ne a dandalolin harsunan Turanci, da Sifaniyanci, da Faransanci, da Larabci, da harshen Rasha, kuma masu bayyana ra’ayoyi 7,431 sun amsa tambayoyin da aka gabatar cikin sa’o’i 24. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp