An sake bankado wasu rahotanni dake zargin aikata cin zarafi na jima’i a rundunar sojojin Amurka, kuma rahotannin sun ce abun da aka gano ya wuce tunani.
Sakamakon kuri’un jin ra’ayin jama’a da kafar CGTN ta gudanar ta yanar gizo, ya nuna kaso 95.01 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyinsu, sun yi matukar damuwa game da munin laifukan cin zarafin da ake zargi na gudana a fannin aikin sojin Amurka, wanda hakan keta hakkin bil adama ne.
- Trump Ya Sha Alwashin Fatattakar Baki Daga Amurka Idan Aka Sake Zaben Sa
- Shugaba Tinubu Ya Amince A Sake Gina Gadar Wagga Da Ta Rushe
Har ila yau, wani bincike da jami’ar Brown ta Amurka ta gudanar ya gano aukuwar irin wadannan laifuka har 73,695 a sashen rundunar sojin ta Amurka a shekarar 2023 kadai, adadin da sau biyu ya ninka 29,000 da ma’aikatar tsaron kasar ta bayyana. Karkashin hakan, kaso 94.21 na masu bayyana ra’ayoyinsu na ganin da gangan gwamnatin Amurka ke boye wannan tsari na cin zarafi ta jima’i a bangaren rundunar sojojin kasar. Kana wasu kaso 93.9 bisa dari na ganin rundunar sojojin Amurka ta rasa kimarta sakamakon wannan lamari.
Kari kan hakan, an samu rahotannin aikata irin wadannan laifuka tsakanin dakarun sojojin kasar ta Amurka a sansanonin kasar dake Japan, da Koriya ta kudu, da karin wasu sansanonin dake ketare.
Alkaluman masu bayyana ra’ayoyinsu sun nuna yadda kaso 93.74 bisa dari suka amince, cewa bayyanar wannan badakala na nuni ga halayyar danniya ta kasar Amurka. (Mai fassara: Saminu Alhassan)