Wani binciken da tashar rediyo ta NPR ta kasar Amurka ta gudanar tare da gidauniyar Robert Wood Johnson da Jami’ar Harvard ya nuna cewa, a cikin Amurkawa baligai fiye da 4000 na kabilu daban daban, wadanda aka gudanar da bincike a kansu, kashi 69 cikin dari na ‘yan kabilun ainihi na kasar, da ake kiransu Indians a Turance, suna fuskantar matsananciyar matsin lamba saboda hauhawar farashin kayayyaki, mafi girman adadin cikin al’ummun kasar Amurka.
Ban da wannan, kashi 58 cikin dari na ‘yan kabilun ainihi na Amurka ba su da isashen kudi don biyan bukatar sayen kayayyakin masarufin da ake bukata cikin wata daya.
A fannin sayen abinci, kashi 40 cikin dari na ‘yan asalin kasar suna fama da matsalar rashin isashen abinci sakamakon talauci. (Mai Fassarawa: Safiyah Ma)