Wani rahoton hukumomin kasar Sin ya bayyana cewa, zuwa karshen shekarar 2021, adadin mutanen dake da inshorar tsoffi a kasar, ya kai kusan biliyan 1.03, wanda ya karu kan miliyan 30.07 da ake da ita a shekarar 2020.
Rahoton wanda hukumar kula da lafiya da ofishin kula da ayyukan da suka shafi tsoffi na kasar suka fitar cikin hadin gwiwa, ya bayyana cewa, kasar Sin na da kusan mutane miliyan 267.37 da suka manyanta, wadanda shekarunsu suka fara daga sittin zuwa sama, inda suka dauki kaso 18.9 na jimilar al’ummar kasar.
A cewar rahoton, zuwa karshen shekarar 2021, kasar Sin na da kimanin mutane miliyan 200.56 da shekarunsu suka kai 65 zuwa sama, kuma daga cikinsu, sama da miliyan 119.41 sun samu hidimomin kiwon lafiya a birane da yankunan karkara.
Har ila yau zuwa karshen baran, akwai cibiyoyin kula da tsoffi 358,000 a fadin kasar, wadanda ke samar da gadaje akalla miliyan 8.16. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp