Allah ya yi rantsuwa da Tauraron Surayya Idan ya buya “Wannajmi iza hawa”. Abokinku – Annabi Muhammad (SAW) bai bata ba “Ma Dalla Sahibukum wa ma Gawa’. Ba ya yin furuci a kan son ransa ‘wama yandiku anil hawa”, face abin da aka yi masa wahayi da ya yi furuci a kansa. “In huwa illa wahyun yuha”. Ubangiji mai tsananin karfin nan shi ya sanar da shi “Allamahu shadidul kuwa”. Wannan kyakkyawan wanda ya daidaita “Zu mirratin fastawa”. Yana nan kan mahudar rana, “Wa huwa bil ufukil A’ala”. Annabi Muhammad (SAW) a nan ya ga Mala’ika Jibrilu (AS). Ya taba ganin shi a Kogon Hira.
Shehu Ibrahim Kaulaha ya kalubalanci Malamai da cewa, in dai sun yarda Manzon Allah ya ga Mala’ika Jibrilu to ya taba ganin Allah, saboda idanun da suka ga Fiffike duba dari shida (600,000) kuma kowanne fiffike daya ya rufe mafitar rana da mafadarta.
- Falalar Ziyarar Kabarin Annabi S.A.W (1)
- LEADERSHIP Ta Jinjina Wa Shehu Isma’ila Mai Diwani Kan Shafin Dausayin Musulunci
Sannan Annabi Muhammad (SAW) ya kusanta ga Rabbi kuma ya sake kusanta, “Summa dana fatadalla”, sai da ta kai ga kusantarshi ta kai kamar tankwaren gwafa ko kuma mafi kusa, “Fa kana kaba kausaini au adna”. Sai ya yi wahyi ga bawansa, abin da ya yi masa wahayi, “Fa auha ila abdihi ma auha”. Zuciyar Annabi Muhammad (SAW) ba ta yi musun abin da ta gani ba, “Ma Kazabal Fu’adu ma Ra’a”. Yanzu za ku dinga jayayya da shi akan abin da ya gani, “A fatumarunahu ala ma yara”. Bayan ya ganshi a wani lokaci ma na daban, “Wa lakad ra’ahu nazlatan ukhra”. A wajen magaryar tikewa, “Inda sidratil muntaha”. Wacce Aljannar Ma’awa take wajenta, “Indaha Jannatul Ma’awa”. Yayin da ya lullube magaryar nan da abin da ya lullube ta, “Iz yagshas sidrata ma yagsha”. Idon Manzon Allah ba ta karkace ba kuma ba ta shige gona da iri ba, “Ma zagal basaru wama daga”. Ya ga daga cikin ayoyin Ubangijinshi mai girma, “Lakad ra’a min ayati rabbihil kubra”. Wadannan ayoyi sun tattaro girma da matsayin Manzon Allah (SAW).
Yana daga cikin darajojin da Allah ya fada na Annabi a cikin Alkur’ani, kiyayewar da Allah ya yi masa daga Mutane. Fadar Allah madaukaki cewa “Ya kai wannan Manzo, isar da abin da aka saukar a gare ka daga Ubangijinka, in ba ka yi haka ba, ba ka Isar da sakon Ubangijinka ba, Allah zai kiyaye ka daga Mutane” (Ya Ayyuhar rasulu ballig ma’unzila ilaika min rabbika, wa illam taf’al fama ballagta risalatahu, Wallahu ya’asimuka minannas…).
Da kuma fadinsa a cikin wata aya ” Ka tuna yayin da wadanda suka yi kafurci suke maka makircin ko su daure ka a cikin daki har mutuwa, ko kuma su kashe ka ko su kore ka daga garinka, suna ta shirya wannan makirci, shi ma Allah yana shirya musu makirci, Allah ya fisu iya shirya makirci” (Wa iz yamkuru bikallazina kafaru liyusbituka au yaktuluka au yakrujuka, wa yamkuruna wa yamkurullah, wallahu kairul makirin.)
Allah ya kara fada cikin wata aya yana cewa “ko ba ku taimake shi ba, to Allah ya taimake shi, yayin da Kafiran Makkah suka fitar da shi, yana dayan biyu, a yayin nan suna cikin kogo yana ce wa sahibinshi kar ka yi bakin ciki, Allah yana tare da mu, sai Allah ya saukar da nutsuwar sa a gare shi, ya kuma karfafe shi da rundunar da ba a ganinta, ya sanya kalmar kafirai ita ce kaskantacciya, Kalmar Allah kuwa ita ce babba, Allah mabuwayi ne, sannan gwani ne.” ( Illa tansuruhu fakad nasarahullahu iz akrajahullazina kafaru saniyas naini iz huma fil gari iz yakulu lisahibihi la tahzan innallah ma’ana, fa’anzalalllahu sakinatahu ala rasulihi wa’ayyadahu bijunudin lam tarauha, waj’ala kalimatallazina kafarus sufla, wakalimatullahi hiyal ulya, wallahu azizun hakim).
Bayan shugabannin kafiran Makkah sun shiga bayan gida sun boye suna ta shirin yadda za su yi da Annabi (SAW), wasu daga ciki suka ce a kore shi, wasu suka ce a kashe shi, sun cimma matsayar kashe shi. Suka zabi matasa 70 daga dukkan kabilun Kuraishawa kowanne a ba shi takobi gaya wa jini-na-wuce kan kashe Annabi, sun yanke shawarar hakan ne kan cewa bani Hashim ba za su iya yakar duk kabilun Kuraishawa ba, a karshe sai dai a biya Banu Hashim diyya.
Amma duk da haka, sai da Allah ya tseratar da shi da fadinsa “Wa ja’alna min baini aidihim Saddan. Wa min khalfihim saddan fa’agshainahum fahum la yubsirun”
Haka nan kuma Allah ya kiyaye shi a kogon hira da ya sa gizo-gizo ya yi saka lokacin da kafiran Makkah suka zo neman shi a kogon don su kashe shi. Sannan kuma Allah ya sanya nutsuwa a cikin zuciyarshi, Allah ya sanya nutsuwa a zukatan Sahabbai gabadaya a lokacin yakin Uhud har Allah yake cewa ” sai muka saukar da nutsuwa a gare ku, har wasu suna gyangyadi a filin yaki…”
Yana daga cikin girman Annabi da Allah yake fada a cikin Alkur’ani, kamar yadda ya ci gaba da cewa: “falam taktuluhum walakinnallaha katalahum – ba kai ka kashe su ba, Allah ne ya kashe su.”
“Wama ramaita iz ramaita walakinnallah rama – ba ka yi jifa ba, yayin da ka yi jifa, Allah ne ya yi.”
“Waliyubliyal Muminina minhu bala’an hasana, Innallaha Sami’un Alim – Ya yi haka ne don ya jarrabi Muminai da jarrabawa Kyakkyawa, Kuma Lallai Allah mai ji ne kuma mai Ilimi ne.”
A wata aya kuma ya ci gaba da cewa: “ Kul ya ayyuhan nasu inni Rasulullahi ilaikum jami’anillazi lahu mulkus samawati wal ardi, la’ilaha illahuwa yuhyi wa yumit, Fa’aminu billahi warasulihin nabiyyil ummiyyilazi yu’uminu billahi wa kalimatihi wattabi’uhu la’allakum tahtadun – Ka ce, ya ku mutanen Makkah ko kuma Mutanen Duniya, lallai ni Manzo ne gare ku baki daya, Allah din nan wanda mulkin sama da kasa duk nasa ne, babu wani Ubangiji sai shi, Kuma shi ne wanda ke rayawa da kashewa, to ku yi Imani da wannan Allah da Ma’aikinsa (wanda) bai taba rubutu da karatu ba amma ya yi Imani da Allah da kalmominsa Alkurani, to ku bi shi ko kwa shiryu.”
Annabi bai taba karatu ko rubutu ba amma ya zo da abin da masu karatu da rubuta ba su taba zuwa da irin sa ba, wannan shi ya tabbatar da cewa Annabi Kur’ani ba na sa ba ne na Allah ne.
Alkadi Iyad Rahimahullahu ya ce: wannan aya tana daga cikin kebance-kebance da Allah ya yi wa Annabinsa Annabi Muhammadu Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi, cewa Allah ya aiko shi ga dukkan al’umma baki daya, su kuma sauran Annabawa an tura su ne kawai ga mutanensu.
Kamar yadda Allah yake cewa: “Wa ma Arsalna min rasulin illa bilisani kaumihi liyubayyina lahum, fayudillullahu man yasha’u wa yahdi man yasha’u wahuwal azizul hakim – Ba mu aiko wani daga cikin ma’aika ba face daga cikin yaran mutanensa don ya yi musu bayani, sai Allah ya batar da wanda ya so da adalcinsa sannan ya shiryar da wanda ya so da falalarsa, Allah mabuwayi ne kuma gwani.”
A wani hadisi, mai tsira da Amincin Allah su tabata a gare shi ya ce: “Bu’istu ilal Ahmari wa Aswadi – An turo ni ga duk wata jar fata da bakar fata”
Allah ya kara fada cikin girman Annabi a wata Aya yana cewa: “Annabiyyu aula bil muminina min anfusihim, wa azwajuhu ummahatum, wa ulul arhami ba’aduhum aula bi ba’adin fi kitabillahi minal muminina wal muhajirin illa an taf’alu ila auliya’ikum ma’arufa, kana zalika fil kitabi masdura – Annabi Muhammadu, shi ya fi ga Muminai a bisa kansu”. Ma’ana muminai sun fi zabar Annabi Muhammadu a bisa kansu, sun ba da rayuwarsu a kansa, Ranar Yakin Uhudu Muminai da yawa sun yi shahada kan kare Annabi Muhammadu. Matayen Manzon Allah Iyaye ne ga Al’ummarsa, haka kuma Annabi shi ma Uban al’ummarsa ne a wani karatu kafin a soke shi.
Shehu Ibrahim Inyass Kaulaha a wajen Tafsiri da ya zo wannan Ayar “Makana Muhammadun aba ahadin min Rijalikum walakin rasulallahi wa khataman nabiyyina…” sai ya ce Allah ya ce Matan Annabi Iyayenmu ne amma me ya sa bai ce Annabi Ubanmu ba ne? sai Shehu yace, sabida in Allah ya ce Annabi ubanmu ne to ba zai yi aure ba kenan, sabida ba zai aure ‘yarshi ba. Don haka matan Annabi bayan rasuwa babu wanda ya aure su sabida Iyayenmu ne.
“Dangi ga sashinsu ya da ce su yi gado a cikin littafin Allah, daga Muminai da Muhajirai, sai dai ba laifi ku yi alheri ga makusantanku, ku ba su wani abu daga cikin gadonku, amma sharadi kar ya wuce daya cikin ukun dukiyar kuma kar wanda za a bai wa ya zama yana da rabo a cikin gadon. Wannan soke tsarin gadon da kuke yi a farko, aka zo da sabo, wannan shi ne a lauhil mahfuzi.
A cikin tafsirin wannan aya, malamai masu tafsiri suka ce “Aula bil muminina” Shi ya fi dacewa daga Muminai, Yana nufin umarnin da Annabi ya zartar, shi ya fi dacewa a wurin Muminai, wasu malamai kuma suka ce bin umarnin Annabi shi ya fi ga Mumini kan bin ra’ayin kansa.
Matayen Annabi cikin hurumci ai kamar iyayenmu ne, ya haramta ga ‘ya’ya su auri iyayensu, to haka ya haramta ga al’ummar Annabi su auri matayensa sabida iyayen al’ummarsa ne cikin hurumci. Allah ya yi haka ne don girmamawa ga Annabi kuma kususiyyarsa ce. Kuma matayen Annabi, matayensa ne a cikin Aljannah amma in wani ya aure su to sun zama matayen wasu a Aljannah.
Duk da cewa, kafin a soke wannan ayar da ana karantata da “Wa azwajuhu ummahatuhum, wa huwa Abun lahum” amma ayar “Ma kana Muhammadun Aba ahadin min rijalikum…” ta soke ta.
Ubangiji madaukakin sarki ya fada yana cewa: “Wa laula fadlullahi alaika warahmatuhu lahammat da’ifatum minhum anyudilluka, wama yudilluna illa anfusahum,wama yadurrunaka min shai’in, wa’anzalallahu alaikal kitaba wal hikmata, wa allamaka malam takun ta’alam, wa kana fadlullahi alaika azima ”. Ma’ana, ba don falalar Allah da rahamarsa a gare ka ba ya rasulullahi, da wata jama’a daga cikinsu sun yi nufin su batar da kai, amma ba kowa za su batar ba sai kansu, ba za su cutar da kai da komai ba, Allah ya saukar maka da Alkur’ani da abin da yake cikin Alkur’ani na daga hukunce-hukunce, kuma ya sanar da kai hukunce-hukunce na daga abin da ka kasance ba ka sani ba, lallai falalar Allah a gare ka na sanar da kai hukunce-hukunce ta kasance mai girma.
Malaman tafsiri suka ce, falalar Allah mai girma ita ce ba ka Annabta, wasu kuma suka ce ita ce abin da Allah ya shirya wa Annabi Muhammadu tun azal, wasu kuma sun tafi a cewa wannan aya tana nuni da cewa lallai Annabi Muhammadu ya ga Allah a daren Isra’i, ita ce falalar da Annabi Musa bai iya daukar ta ba.