Cutar kwalara a Nijeriya ta yi sanadin mutuwar mutane 103, yayin da sama da mutane 3,000 da ake zargin sun kamu da cutar.
Babban Daraktan Cibiyar Dakile Cututtuka ta Kasa (NCDC), Jide Idris, ya tabbatar da alkaluman a wani taron manema labarai da aka yi a Abuja a ranar Talata.
- Majalisar Dokokin Kano Ta Samar Da Sabuwar Dokar Sarakuna Masu Daraja Ta Biyu
- Zargin Karkatar Da Biliyan 2.8: Gwamnatin Kano Ta Maka Sule Garo Da ‘Yan Uwansa Biyu A Kotu
Ya kara da cewa, a yanzu an samu cutar a kananan hukumomi 187 a cikin jihohi 34 da Babban Birnin Tarayya, Abuja.
A cewarsa, manyan jihohin da aka fi kamuwa da cutar su ne Legas, Bayelsa, Abiya, Ebonyi, Katsina da kuma Jihar Zamfara.
Ya danganta bullar cutar da ambaliyar ruwa da aka samu a wasu jihohi a fadin kasar nan tare da cin gurbataccen abinci da ruwa da kuma bayan gida.
Ya shawarci ‘yan Nijeriya da su kasance masu tsafta tare da yin taka tsan-tsan da cututtuka a lokacin damina.