Hukumar Daƙile Cututtuka Masu Yaɗuwa ta Ƙasa (NCDC), ta ce mutum 14 sun rasu sakamakon kamuwa da cutar kwalara a cikin makonni biyar da suka gabata.
A cewar rahoton da hukumar ta fitar ranar Talata, ana zargin aƙalla mutum 886 sun kamu da cutar tsakanin 27 ga watan Janairu zuwa 2 ga watan Fabrairu 2025.
- Majalisa Ta Yi Watsi Da Kara Akan Akpabio Kan Zargin Neman Yin Lalata Da Natasha
- Janar Tiani Ya Fara Sabon Mulkin Shekaru Biyar A Nijar
An samu ɓullar cutar a jihohi 22 da kuma ƙananan hukumomi 44.
Jihar Bayelsa ce tafi yawan masu waɗanda ake zargin sun kamu da cutar da mutum 695, sai Jihar Ribas da mutum 54, sannan Jihar Neja da mutum 33.
Jihohin Sakkwato, Yobe, Borno, Katsina da Adamawa kuwa sun bayar da rahoton mutum guda kacal da ake tunanin ya kamu da cutar.
NCDC, ta ce yawan masu kamuwa da cutar a bana ya fi na shekarar da ta gabata, inda a lokacin aka samu mutum 506 kacal.
Hukumar ta shawarci al’umma suke shan sha ruwa mai tsafta, su riƙa wanke hannu da sabulu, su ci abinci mai kyau, tare da tabbatar da tsaftar muhalli don guje wa kamuwa da cutar kwalara.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp