Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da rasuwar babban mataimaki na musamman ga gwamnan Kano, kan harkokin rediyo, Abdullahi Tanka Galadanchi.
Sanarwar da daraktan yaɗa labarai na fadar gwamnatin Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ta bayyana cewa Galadanchi, ya rasu ne a yau Laraba a Asibitin Koyarwa na Aminu Malam Kano bayan gajeriyar jinya.
- Kwalara Ta Kashe Mutum 14, Ana Zargin 886 Sun Kamu A Nijeriya – NCDC
- Janar Tiani Ya Fara Sabon Mulkin Shekaru Biyar A Nijar
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya nuna alhininsa kan rasuwar, inda ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai ƙwazo da jajircewa wanda ya bayar da muhimmiyar gudunmawa a fannin yaɗa labarai da sadarwa a gwamnatinsa.
”Rasuwar Abdullahi Tanka Galadanchi babban rashi ne ga gwamnatinmu da al’ummar Kano gaba ɗaya,” in ji sanarwar.
Gwamnan ya kuma miƙa ta’aziyyarsa ga iyalansa da abokan aikinsa, inda ya yi addu’ar Allah ya jiƙansa da rahama.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp