An samu barkewar cutar amai da gudawa a karamar hukumar Kirikasamma ta Jihar Jigawa, wanda ta yi sanadin mutuwar mutane bakwai, yayin da aka kwantar da wasu da dama a asibiti.
Shugaban kula da lafiyar al’umma na yankin, Musa Abdullahi Diladige ne, ya tabbatar da barkewar cutar a yankunan Malori, Maikintari, Dilmari, Kirikasamma, da wani bangare na kauyen Baturiya.
- Dangote Ya Ceto Nijeriya Daga Durƙushewa – Odetola
- Mataimakin Shugaban Sin Ya Gana Da Firaministan Jamhuriyar Nijar
Diladige, ya bayyana cewa wadanda abin ya shafa na fama da alamomin rashin lafiya masu tsanani kamar gudawa, kumburin ciki, amai, da zazzabi.
An tura ma’aikatan lafiya zuwa yankunan don samar da agajin gaggawa.
Hukumomi sun dauki matakin gaggawa ta hanyar sayan magungunan da ake bukata don fara jinyar masu cutar.
Daraktan gudanarwa da ayyukan gama-gari, Idris Gambo Abubakar, ya yi alkawarin bayar da goyon bayan da ake bukata don dakile yaduwar cutar.
Ana kyautata zaton ruwan sama mai tsanani da aka samu a yankin ne ya haifar da barkewar cutar, inda gine-gine suka lalace kuma hanyoyin samar da ruwa suka lalace.
An shawarci mazauna yankin da su dauki matakan kariya nan take.
Daga cikin matakan akwai tsaftar jiki, guje wa abinci da ruwa marasa tsafta, da kuma neman kulawar likitoci idan aka lura da alamomin rashin lafiya.