Kwalejin Kimiyya ta Jihar Adamawa ta yaye tare da amsar sabbin dalibai 133 a tsangayoyi digiri daban-daban.
Shugaban makarantar Farfesa Muhammad Dahiru Toungos, ya bayyana haka lokacin da yake jawabin maraba da baki, a bikin amsar sabbin daliban da aka yi ranar Asabar a makarantar.
- Dan Nijeriya Ya Kafa Tarihi A Gasar Siriya A Daga Afirka
- Sakarci Da Talauci Ne Yasa Gwamnatin Zamfara Shiga Gidana Sata- Bello Matawalle
Shugaban, ya kuma gargadi daliban da su mayar da hankali ga karatu, da nisantar dabi’un da zai dakushe kima da darajar makarantar.
Haka kuma makarantar ta yi hadin gwiwa da Jami’ar Maiduguri, domin gudanar da tsangayoyin digirin digirgir a bangarori bakwai.
Da yake jawabi, mataimakin shugaban Jami’ar Maiduguri, Farfesa Aliyu Shugaba, ya jaddada matsayin jami’ar wajan samar da mafi ingancin karatu ga dalibai.
Don haka ya bukaci sabbin daliban da su nuna kwazo da sadaukarwa domin su zama kyakkyawan abin koyi kuma misali ga makarantar.
Shi ma shugaban makarantar koyon aikin noma da ke Ganye, Hussaini Idris Danjuma, jan hankali ya yi wa iyayen yara, ya ce “makarantar farko daga gida ta ke, ya kamata iyaye su kula da tarbiyar ‘ya’yansu kafin zuwansu makaranta.
“Kyakkyawar karantarwa, tana samuwa da kyakkyawar tarbiyya daga gida, wannan shi muka sani a al’adunmu, iyaye su lura da wannan” in ji Idris.