Kwamandojin ‘yan ta’addar Boko Haram hudu da wasu mayaka 13 da ‘yan uwansu 45 sun mika wuya ga dakarun hadin gwiwa na kasa da kasa (MNJTF).
Sanarwar da Kakakin Rundunar MNJTF, Laftanal Kanal Abubakar Abdullahi ya fitar, ya ce matakin ya biyo bayan yadda rundunar hadin gwiwa ta ke ci gaba da gudanar da ayyukan yaki da ta’addanci.
Ya ce tsakanin ranakun 14 zuwa 15 ga watan Agustan 2023, “manyan kwamandojin Boko Haram hudu, manyan mayakan 13, da kuma ‘yan uwansu 45, sun ajiye makamansu tare da mika wuya ga dakarun sashe 3 na MNJTF.”
Bugu da kari, a ranar 15 ga Agusta, 2023, wasu kwamandoji biyu da mayaka hudu da ’yan uwansu 24 sun mika wuya.
Ya ce ‘yan ta’addan da suka mika wuya sun mika bindigoginsu kirar AK-47 guda biyu, harsashi 99.
Ya nanata cewa MNJTF na ci gaba da jajircewa wajen karfafa zaman lafiyar yankin tafkin Chadi.