Kwamishinan kananan hukumomi da masarautu na jihar Bauchi, Ahmed Jalam (Mai kankana) ya rasu.
Jalam ya rasu ne a wani mummunan hatsarin mota da ya afku a hanyar Bauchi zuwa Misau ranar Asabar.
- Abdul Hamid Dbeibah: Ina Fatan Zurfafa Dangantakar Dake Tsakanin Kasashen Libya Da Sin
- Ali Nuhu Ya Gabatar Da Lacca Kan Fina-finan Nijeriya A Faransa
Mai baiwa gwamnan jihar Bauchi shawara ta musamman kan harkokin yada labarai, Mukhtar Gidado, ya tabbatar da rasuwar Jalam a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai.
Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya bayyana matukar alhininsa game da rasuwar hadimin nasa wanda ya aminta da shi matuka.
Bala a cikin sakon ta’aziyyar da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Lawal Muazu Bauchi ya raba wa manema labarai, ya ce rasuwar Jalam ba zato ba tsammani ta jefa jihar cikin jimami, domin ya shahara da jajircewa wajen gudanar da ayyukan gwamnati da kuma sadaukar da kai ga gwamnati.
Ya roki Allah Madaukakin Sarki da ya gafarta kura-kuran Jalam ya kuma sanya Aljanna ta zamo makomarshi.
LEADERSHIP ta samo cewa, za a yi jana’izar Jalam a ranar Lahadi a mahaifarsa, da ke cikin karamar hukumar Dambam a jihar.