A halin yanzu ana ci gaba da gudanar da bikin baje-kolin kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin karo na shida wato CIIE a birnin Shanghai dake gabashin kasar Sin, inda kwamishinan kula da harkokin cinikayya da zuba jari na yankin Asiya daga karamin ofishin jakadancin tarayyar Najeriya dake Shanghai, Ibrahim A. Ahmed ya yaba matuka da manufofin kasar Sin na fadada bude kofa ga kasashen waje, da kara shigo da kayayyaki daga kasashe daban-daban.
Wakilinmu Murtala Zhang dauke da karin bayani daga Shanghai.
- Wakar Kidaya: Aisha Humaira Ta Nemi Al’umma Su Daina Tsangwamar Mawaki Rarara
- Dandalin Hongqiao Na Maida Hankali Ga Kiyaye Tsarin Cinikayyar Sassa Daban Daban
Malam Ibrahim Ahmed ya ce, Najeriya na farin-cikin samun damar halartar bikin CIIE a wannan karo, ganin yadda yake samar da muhimmiyar dama ga tallata kayayyakin kasar, musamman amfanin gona da albarkatun kasa, inda ya ce:
“Tun fara bikin na bana, mutane da yawa sun zo nan don tambayar kayayyakinmu har sun yi odar wasu da dama. Mutane suna sha’awar kayayyakin Najeriya, wadanda suka bambanta da na sauran kasashen Afirka sosai. Kayayyakin Najeriya na da inganci sosai, kuma ina matukar farin-cikin ganin cewa suna samun karbuwa a wajen mutanen China.”
Jami’in ya kara da cewa, kasar Sin ba ta taba barin kasashen Afirka a baya ba wajen samar da ci gaba, ganin yadda bikin CIIE din ke samar da wata muhimmiyar dama ga kasashen Afirka wajen raya harkokin kasuwanci, inda ya ce:
“Ya samar mana da damar mu’amala da masu zuba jari na kasar Sin, al’amarin dake da muhimmanci ga ci gaban tattalin arzikin Najeriya. Don haka muna godiya ga gwamnatin kasar Sin saboda damar da ta samar mana wajen tallata kayayyakinmu a wannan bikin.”
Malam Ibrahim Ahmed ya yi karin haske cewa, Najeriya ta cimma nasarori da dama wajen halartar bikin CIIE tun daga irinsa na farko da aka yi a shekara ta 2018, kuma a bana, yana son tallata wasu muhimman nau’o’in amfanin gona, musamman gyada, da ridi, da busasshiyar citta, da sauran wasu albarkatun ma’adinai.
Da ya tabo batun burin da Najeriya take son cimmawa a wajen bikin CIIE na bana, jami’in ya ce:
“Muna fatan ganin kamfanoni da ’yan kasuwanmu kanana da matsakaita sun samu damar tallata kayayyakinsu da kyau, don kara samun ci gaban sana’o’insu.” (Murtala Zhang)