Babbar Kwamishanar Kidaya ta Nijeriya, Hajiya Saa Dogonbauchi ta sadaukar da albashinta na tsawon shekara guda ga matan Karamar Hukumar Kaduna ta Kudu.
Babbar Kwamishanar ta bayyana haka ne a lokacin da take raba buhunan shinkafa kimanin 3,000 ga al’ummar Karamar Hukumar Kaduna ta Kudu a Jihar Kaduna.
Ta ce za ta tara albashinta ta siyo kayayyakin sana’oi ta raba ga mata domin taimaka musu dogaro da kawunansu.
Wasu daga cikin mutanen da suka amfana da rabon shinkafar sama da 5,000 da suka kunshi maza da mata, musulmi da kirista da masu bukata ta musamman daga mazabu 13 na karamar hukumar ta Kaduna ta Kudu don gudanar da bikin Sallah cikin farin ciki, sun bayyana jin dadinsu da wannan karamci tare da addu’oi a gare ta.
“Muna godiya da jinjina ga mai girma Shugaban KasaAsiwaju Bola Ahmed Tinibu da ya zaba mana ‘yar kasa tagari mai kishin mutane a matsayin Kwamishinar Hukumar Kidaya, tabbas idan mutane masu rike da mukami suna tallafa wa al’umma irin haka za a samu sauki ta fannoni da dama. Hajiya Sa’adatu Garba Dogonbauchi muna addu’ar Allah ya yi miki sakayya da Gidan Aljanna ya kara kai matsayi gaba.” In ji wasu da aka zanta da su a wurin rabon abincin.