Kwamitin bincike da Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kafa domin bincikar Kwamishinan Sufuri na jihar, Ibrahim Namadi, kan tsaya wa wani da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi, Sulaiman Aminu Danwawu, ya kammala aikinsa kuma ya mika rahoto ga gwamnatin jihar.
Shugaban kwamitin, kuma mai bai wa Gwamna shawara na musamman kan harkokin shari’a da kundin tsarin mulki, Aminu Hussain, ya miƙa rahoton ne a ranar Litinin ga Sakataren Gwamnatin Jiha (SSG), Umar Farouk Ibrahim. Ya bayyana cewa kwamitin ya gudanar da cikakken bincike bisa gaskiya, da hujjoji, ba tare da son rai ba.
- Gwamnatin Kano Za Ta Mayar Da Gidan Gyaran Hali Na Kurmawa Gidan Tarihi
- Yadda Kwamishinan Kano Ya Karɓi Dala $30,000 Domin Yin Belin Dilan Ƙwaya A Kotu – Rahoto
Hussain ya ce an tattauna da Kwamishinan Sufuri, wanda ya miƙa bayanansa ta rubutu, sannan kuma an yi hira da wasu muhimman mutane da suka shafi lamarin, ciki har da Abubakar Umar Sharada, mai taimaka wa gwamna kan farfado da siyasa, da Musa Ado Tsamiya, mai taimakawa gwamna kan magudanan ruwa.
Kwamitin ya kuma nemi bayanai daga hukumomin tsaro da shari’a irin su Hukumar Tsaro ta DSS, hukumar NDLEA da kuma ƙungiyar lauyoyi ta NBA domin tabbatar da sahihanci da cikakken bincike. Hussain ya ce sun duba takardun hukuma da suka dace tare da bin dokoki da ƙa’idojin aikin bincike.
Da yake karɓar rahoton a madadin gwamnatin jihar, SSG Umar Farouk Ibrahim ya jinjina wa kwamitin bisa kwazo da kishin aiki, yana mai cewa “Gwamnatin Kano za ta nazarci rahoton kwamitin sannan ta ɗauki matakin da ya dace bisa abubuwan da aka gano da shawarwarin da aka bayar.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp