Hukumar JAMB ta karɓi rahoto daga Kwamiti na Musamman kan maguɗin Jarabawa (SCEI) wanda ya gano yadda amfani da fasaha ke lalata tsarin karɓar ɗalibai a Nijeriya.
Shugaban kwamitin, Dakta Jake Epelle, ya bayyana a Abuja cewa binciken ya gano hanyoyin “finger blending” guda 4,251 da kuma magudin da ya dogara da AI guda 190 ta hanyar “image morphing” a jarabawar UTME ta 2025.
- Likitoci Sun Fara Yajin Aikin Gargaɗi Na Mako Ɗaya A Abuja
- JAMB Ta Kaddamar Da Kwamitin Bincike Kan Satar Jarabawa
Kwamitin, wanda aka kafa a ranar 18 ga Agusta 2025, ya kuma gano masu cewa suna da nakasar ƙarya har 1,878, da wanda suka bayar da shaidun ƙarya, da masu rajistar NIN sau da dama, da kuma haɗin baki tsakanin ɗalibai da masu shirya magudi. Epelle ya ce lamarin ya zama tsari ne shiryayye na zamani kuma an saba da shi, inda iyaye, makarantun koyar da jarrabawa, wasu makarantun sakandare, da ma cibiyoyin CBT suke da hannu.
Kwamitin ya ba da shawarar amfani da AI wajen gano masu ƙarya a bayanan yatsu, da kafa Cibiyar Tsaro ta Jarabawa ta Ƙasa, da kuma ɗaukar matakai masu tsauri kamar soke sakamakon magudi, da haramta shiga jarabawa na tsawon shekara ɗaya zuwa uku, da gurfanar da masu laifi tare da kafa rajista ta musamman ta hukunci da za a rika amfani da ita a makarantu da wuraren aiki.
Haka kuma, an ba da shawarar yin gyaran dokar da ta kafa hukumar JAMB da dokar satar jarrabawa don haɗa laifukan dijital da na fasaha, tare da kafa sashin shari’a a JAMB.
Kwamitin ya kuma jaddada buƙatar wayar da kan jama’a da kamfen ɗin mutunta kai, da haɗa ɗabi’a mai kyau a cikin kundin karatu, da ɗaukar iyaye da ke taimaka wa ‘ya’yansu wajen magudi a matsayin masu laifi.
Kwamitin ya gargadi cewa idan ba a ɗauki mataki cikin gaggawa ba, za a ci gaba da lalata ingancin tsarin ilimi a Nijeriya, abin da zai karya harsashin ci gaban ɗan Adam da tattalin arziki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp